Manyan kungiyoyin kwallon kafa na kasar Ingila Manchester City da Arsenal sun buga kunnen doki a wasan mako na 30 na gasar Firimiya da suka buga a filin wasa na Etihad da ke Birnin Manchester.
An yi tsammanin wasan tsakanin kungiyoyin Manchester City da arsenal ya yi zafi duba da cewa dukkansu suna fatan ɗarewa saman teburin Firimiya na bana yayinda ake gab da kammalawa.
Amma kowane bangare ya jajirce domin ganin ya hana abokin karawarsa jefa kwallo ko ɗaya a ragarsa, inda hakan kuma ya sa Liverpool ta koma matsayi na daya a kan teburin gasar bayan ta doke Brighton a Anfield.
A wani labarin na daban an cafke wasu mutane uku kan laifin satar raguna 132 a karamar hukumar Mashegu da ke Jihar Neja.
Wadanda ake zargin dai sun hada da Mohammed Abdullahi Chumo mai shekaru 30, Aliyu Salihu mai shekaru 20 da kuma Arzika Ahmadu mai shekaru 25.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya ce wadanda ake zargin sun amsa laifin ne lokacin da aka yi musu tambayoyi.
Ya bayyana cewa sun hada baki tare da sace raguna 132 a unguwar Manigi da ke karamar hukumar Mashegu.
“Abin farin ciki, a ranar 14 ga watan Maris, 2024, mai ragunan da aka yi satar, ya hangi wani da raguna guda shida daga cikin wadanda aka sace yana kokarin sayar da su,” in ji Abiodun.
Duba nan: Dakatar Da Wasu ‘Yan Majalisu A Zamfara
Ya bayyana cewa, nan take aka kama wanda ake zargin sannan ya jagoranci tawagar ‘yansanda