Wani kwararren likita a fannin da ya shafi zuciya da hanyoyin numfashi Sanjay Sharma, ya ce mai yiwuwa dan wasan tsakiya na kasar Denmark Christian Eriksen ba zai sake buga kwallon kafa ba har abada.
Ana tsaka da wasan da kasar sa Denmark ke karawa da Finland na gasar cin kofin kasashen Turai ta Euro 2020 a ranar Asabar da ta gabata, Eriksen ya yanke jiki ya fadi sakamakon tsayawar bugun zuciya da kuma daukewar numfashi.
Dan wasan dake taka leda a kungiyar Inter Milan ya tsallake rijiya da baya, sakamakon taimakon gaggawar da abokan wasansa suka bashi akan fili, kafin isowar jami’an lafiya a yayin da ‘yan kallo da sauran ‘yan wasa da jami’ai ke kallo cikin kaduwa, bayan farfadowarsa ne kuma aka garzaya da shi asibiti, inda har yanzu yake kwance cikin yanayi mai kyau kamar yada hukumar kwallon kafa ta Denmark ta sanar.
Sai dai Dakta Sharma, wanda Farfesa ne da ya kware a fannin likitancin kula da zuciya da hanyoyin numfashi wanda yayi aiki tare da Chrisrtien Eriksen a kungiyar Tottenham ya ce dan wasan na bukatar sa’a babba kafin samun damar komawa fagen kwallo kamar yadda ake bukata, la’akari da tsauraran dokokin kungiyoyi da hukumomin kwallon kafa, baya ga ma batun sake samun lafiyar sa.
Wasan kwallon kafa nacikin wasanni masu matukar farin jini musamman a wajen matasa dama wasu tsofaffin.
Wasa ne daya fi kowanne nau’in wasa shahara nahiyar afrika, turai har ma da asiya amma abinda ya zama abin tambaya a wajen masu hankali da tunani shine menene fa’idar goyon bayan kungiyoyin kasashen turai da matasan musulmi keyi?