Rahotanni Ingila sun tabbatar da cewa cinikin dan wasa Harry Maguire zuwa West Ham United ya samu cikas.
Tun a satin da ya gabata ne dai Manchester United ta amince da siyar da dan wasan domin komawa West Ham da buga wasa a kan kudi fam miliyan £30.
Sai dai sakamakon rashin cimma matsaya tsakanin dan wasan da Manchester United wajen biyansa wasu kudinsa da ya kamata sakamakon rage albashinsa da zai yi ya sa West Ham ta ga ba za ta iya jira har sai Maguire da United sun daidaita ba.
Dan wasan dai yana daukar fan dubu 190 a duk sati sai dai sakamakon zuwa kofin zakarun turai da Man U ta yi albashin ya karu zuwa fan dubu 200.
West Ham dai za ta ci gaba da neman wasu ‘yan wasan bayan sai dai duk da haka ba ta hakura da Maguire ba idan har dan wasan zai iya cimma matsaya da Man United.
Source: LeadershipHausa