Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta sake yin abin da ta saba, yayin da ta lashe kofin gasar zakarun turai a karo na 15 a gaban magoya baya fiye da 60,000.
Wasan gasar na karshe an buga shi ne a babban filin wasa na Wembley da ke birnin Landan.
Wasan wanda ya matukar kayatarwa ya nuna yadda giwaye biyu a fagen kwallon kafa suka nuna kwarewa da jajircewa a mintuna 45 na farkon wasan, wanda ya kare ba tare da an jefa kwallo a raga ba.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci mataimakin kyaftin din Real Madrid, Dani Carvajal ya jefa kwallo a ragar Dortmund a minti na 74, kafin Vinisius JR ya jefa ta biyu a minti na 82.
Real Madrid ta lashe kofin Zakarun Turai a karo na 15 a tarihinta wanda kuma babu wata kungiya a duniya da ta taba kafa irin wannan tarihi da suka kafa a fagen tamola.
A wani labarin na daban Cristiano Ronaldo ya fashe da kuka bayan da Al-Nassr ta yi rashin nasara a hannun Al-Hilal a wasan ƙarshe na cin Kings Cup a daren Juma’a.
Wasan dai ya yi matuƙar bayar da mamaki amma an tashi 1-1 bayan ƙarin lokaci, Al-Hilal ta samu nasara da ci 5-4 a bugun daga kai sai mai tsaron gida duk da wasa da ƴan wasa tara, Al-Nasr ba ta iya samun nasarar a kan su ba.
Ronaldo, wanda ya ci wa Al-Nasr ƙwallaye uku 58 a wasanni 64 tun lokacin da ya koma ƙungiyar a watan Janairun 2023, an gan shi yana hawaye yayin da ake yi masa jaje.
Wasan wanda aka gudanar a Jiddah, ya ƙunshi jan kati uku da kuma lokuta masu zafi kamar za a yi rigima. Tsohon dan wasan Fulham Aleksandar Mitrovic ne ya ci wa Al-Hilal kwallon da wuri, kuma ɗan wasan Al-Nassr Ayman Yahya ya farke ƙwallon a ƙarshen wasan.
Ronaldo ya samu nasarar cin bugun daga kai sai mai tsaron gida. Daga karshe dai mai tsaron ragar Al-Hilal Yassine Bounou ya yi nasara tare kwallo.
DUBA NAN: Yan Achaba Sun Kai Hari Ofishin ‘Yan Sanda A Legas
Ronaldo ya kafa tarihi a kakar wasa ta bana a Saudi Pro League, inda ya zura ƙwallaye 35, amma kuma ya kare ba tare da ya ci wa Al-Nassr kofi ba, kofin da ya lashe a kakar wasanni ta bara shi kofin zakarun kulob-kulob na Larabawa a Saudiyya.