Shugaban Kasar Brazil, Lula Luiz Da Silva, Ya Bukaci a gaggauta kawo karshen kalaman wariyar launin fata a wasannin kwallon kafa musamman a Turai.
Shugaba Lula ya bayyana haka a shafinsa na twitter, cewar kalaman wariyar launin fata ba za su haifar da da mai ido ba matukar ba’a bar su ba.
jawabin shugaban ya zo ne bayan magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Valencia sun furta kalaman wariyar launin fata akan dan wasan Brazil mai taka leda a Real Madrid, Vinicius Jr.
Alkalin wasa Ricardo Burgos, ya tsayar da karawar bayan an yi masa korafi akan magoya bayan Valencia inda suka dinga jifa suna furta kalaman da basu dace ba akan dan wasan, kuma daga baya ya ba shi katin kora bayan ya bugi dan wasan Valencia, Hugo Duroc, da kusurwar hannunsa.
Shugaban na Brazil ya kara da cewa dole a gaggauta dakatar da faruwar hakan a nan gaba.
A wani labarin na daban jiya ne, mai dakin shugaban kasar Xi Jinping, Peng Liyuan, ta gana da Rosângela Lula da Silva, uwargidan shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Uwargida Peng ya ce, duk da nisan da ke tsakanin kasashen biyu wato Sin da Brazil, al’ummomin kasashen biyu suna da zuciya daya, kuma suna jin dadin hadin gwiwa da mu’amalar al’adu daban-daban.
Peng ya gabatarwa Rosângela tarihi da al’adun kasar Sin, da kuma kyawawan fasahohinsu daban-daban. Ta kuma yi fatan cewa, Lula da Rosângela za su ji dadi tare da samun sakamako mai kyau a ziyarar da suka kawo, tare da fatan karfafa abota mai dorewa a tsakanin kasashen biyu.
A nata bangare kuwa, uwargida Rosângela ta godewa shugaba Xi da mai dakinsa Peng, bisa karramawar da suka yi mata, tana mai cewa, ko da yake wannan ita ce ziyararta ta farko a kasar Sin, amma ta riga ta ji cewa, kasar Sin kasa ce mai dogon tarihi da kyawawan al’adu gami da kuzari na zamani. Ta bayyana aniyarta ta zurfafa fahimtar kasar Sin da inganta hadin gwiwar abokantaka a tsakanin kasashen biyu. (Ibrahim)