Romelu Lukaku da ke taka Leda kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan a matsayin aro daga Chelsea ta Ingila ya tabbatarwa Duniya cewar ba zai tafi Saudia da ake alakanta shi da zuwa ba inda ya kara da cewar yana jin dadin zamansa a Turai.
Lukaku wanda ya buga wasanni a Everton Chelsea Manchester United da kuma Inter Milan ya fadi hakane bayan tashi wasan da kasarsa ta Belgium tayi kunnen doki da kasar Estonia inda shine ya farke wa Belgium kwallon da aka jefa mata bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
Sakamakon jinyar da kyaftin din tawagar Kasar ta Belgium Kevin De Bruyne ke yi Lukaku shi ya jagoranci tawagar a fafatawar da suka tashi canjaras da kasar ta Estonia.
Lukaku ya Kara da cewar duk da yasan manyan yan wasa daga Turai sun koma Saudia da taka leda amma shi bai shirya komawa kasar ba inda ya Kara da cewar akwai gudunmuwar da zai bayar har yanzu.
Zaman aron da Lukaku keyi a Inter Milan yazo karshe yayinda yanzu yake a matsayin dan wasan Chelsea duk da rahotanni sun nuna cewar Inter na tattaunawa da Chelsea don ganin ya cigaba da zama a San Siro a mataki na din din din.