Ɗan wasan Nijeriya Ademola Lookman ya zura ƙwallaye uku a ragar Bayer Leverkusen a wasan ƙarshe na gasar Uefa Europa League da suka buga a filin wasa na AVIVA Stadium dake birin Dublin a ranar Laraba.
Wannan shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen da Xabi Alonso ke horaswa ta yi rashin nasara a hannun wata ƙungiya a kakar wasanni ta bana, inda ta buga wasanni 49 ba tare da an doketa ba.
Kwallaye ukun da Ademola Lookman tsohon ɗan wasan Aston Villa ya jefa a ragar Leverkusen yasa ya zamo baƙar fata na farko da ya taɓa zura adadin waɗannan ƙwallayen a wasan karshe a wata gasa a ƙasar Turai.
A wani labarin na daban shararren dan wasan tsakiyar Real Madrid da Kasar Jamus, Toni Kroos, ya bayyana cewar zai yi ritaya daga kwallon kafa da zarar an kammala gasar Euro ta 2024.
Dan wasan ya shafe shekaru 10 a Real Madrid tun bayan da kungiyar ta saye shi a shekarar 2014 daga Bayern Munich.
Tuni Real Madrid ta fitar da sanarwa a shafinta ja Intanet, inda ta yi wa dan wasan godiya da jinjina kan tsawon lokacin da ya shafe a kungiyar tare da kafa tarihi.
A wannan shekara an sha kai ruwa kan batun ko dan wasan zai sake rattaba hannu a kungiyar don ci gaba da zama kamar yadda Luka Modric ya yi.
Duba Nan: Masu Binciken Tsohon Gwamnan Kano Ganduje Sun Fara Zama
Sai dai daga karshe, Kross ya zartar da hukuncin kan jingine takalmansa da zarar an kammala gasar Euro ta bana.