Ranar Laraba kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta yi nasarar doke abokiyar hamayyarta wato Burnley da ci 3-0 a wasan mako na 37 da suka fafata a gasar Premier a filin wasa na Turf Moor.
Liverpool ta ci kwalln farko ta hannun Roberto Firminho sauran minti biyu su je hutun rabin lokaci sannan Nathaniel Phillips ya ci wa kungiyar kwallo ta biyu ana tsaka da wasa a zagaye na biyun.
Liverpool ta ci ta uku ne ta hannun dan wasan Ingila, Aled Odlade-Chamberlain saura minti biyu a tashi daga fafatawar hakan yasa da wannan sakamakon wasan Liverpool ta zama ta hudu a kan teburi da maki 66 iri daya da na Leicester City wadda ta koma ta biyar kawo yanzu.
Chelsea ce a mataki na uku mai maki 67 da tazarar maki hudu tsakaninta da Manchester United ta biyu ita kuwa Burnley ta yi kasa zuwa mataki na 17 a kasan teburi da maki 39, bayan da tuni Fulham da West Brom da kuma Sheffield United za su buga Championship a badi.
Wasannin karshe a Premier da za’a buga ranar 23 ga watan Mayu:
Arsenal da Brighton & Hobe Albion
Aston billa da Chelsea
Fulham da Newcastle United
Leeds United da West Bromwich Albion
Liverpool da Crystal Palace
Manchester City da Eberton
West Ham United da Southampton
Leicester City da Tottenham
Sheffield United da Burnley
Wolberhampton Wanderers da Manchester United
Tare da matsalar yaduwar cutar duniya ta korona biros a yammacin turai amma dai an cigaba da gabatar da wasanni a nahiyar ta turai.