Shugaban gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Joan Laporta ya ce ba zai ajiye aikin shugabancin kungiyar ba, domin abin da shugaban kula da La liga, Jabier Tebas ya ke fata kenan.
Ranar Litinin Tebas ya ce ya kamata Laporta ya yi murabus idan har ya kasa fayyace wasu kudi da aka biya Jose Maria Enrikuez Negreira, tsohon shugaban kwamitin alkalan wasa a Sifaniya.
A hirar sa da manema labarai akan ko zai ajiye aikin shugabancin kungiyar, Laporta ya ce wannan hukunci ne daga wajen mambobi kan shugabansu, saboda haka sai abinda suka yanke.
An zabi Laporte da yawan rinjaye a watan Maris din shekara ta 2021 kuma zuwan sa kungiyar ya kawo gyara sosai musamman wajen siyo ‘yan wasa da kuma daukar Dabi a matsayin mai koyarwa.
Takaddama ta tashi ne ranar Larabar da ta gabata kan biyan fam miliyan 1.2 ga kamfanin Negreira tsakanin 2016 zuwa 2018 sannan daga baya aka bankado cewar kungiyar ta biya mai shekara 77 kudi yuro miliyon 7 tsakanin shekarar 2001 zuwa 2018, shekarar da ya bar mukamin shugaban kwamitin alkalan wasa na Sipaniya.