Kungiyar Kwallon Kafa Ta Real Madrid Ta Lashe Babbar Gasar La Liga Ta Spaniya Karo Na 35.
Real Madrid ta cimma wannan tarihi ne bayan da ta doke Espanyol 4-0 a yammacin Asabar a filin wasa na Santiago Bernabéu. Kuma an sallama wa Real kofin ne duk da cewa saura wasa huɗu a kammala gasar.
Daga cikin wasannin da suka rage wa Real har da na hamayar birnin Madrid tsakaninta da Atletico. Sai kuma tsakaninta da Levente da Cadiz da Real Betis.
Hakan na nufin mai horar da kungiyar ta Madrid Carlo Ancelotti ya kafa tarihi a matsayin koci ɗaya tilo da ya lashe gasar league a manyan ƙasashen Turai biyar.
Ya ci gasar Serie A a AC Milan, da Ligue 1 a PSG, da Premier League a Chelsea, da kuma Bundesliga a ƙungiyar Bayern Munich.
READ MORE : Jami’an tsaro A Sudan Sun Tarwatsa Masu Zanga-zanar Cika Shekaru 3 Da Kisan Gilla Da Aka yi A Kasar.
Kwallaye biyu da matashin ɗan wasa Rodrygo ya ci, da Kwallon Asensio, da kuma ta Benzema su ne suka bai wa Real Madrid nasara, da ma tun kafin wasan, Madrid ta na neman maki ɗaya ne kacal ta dauke kofin.
READ MORE : Harin Bomb Da Aka kai a Birnin Kabul Yayi Sanadiyar Mutuwar Mutane 5 Tare Da Jikkata Wasu Da Dama.