Kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, ta sake kama hanyar yiwuwar zama zakarar La liga a bana bayan shafe shekaru 7 ba tare da kai kofin gidanta ba, inda ta sake jan tazara tsakaninta da Kungiyoyin Real Madrid da Barcelona wadanda suka shafe shekaru suna lashe kofin.
Atletico bayan nasararta kan Real Sociedad a jiya, yawan tazarar da ke tsakaninta da Barcelona wadda ke gurbin ta biyu a teburin gasar ya zama maki 4, yayinda ita kuma Barcelonar ke da tazarar maki daya tal tsakaninta da Real Madrid kuma Madrid din na da kwantan wasa guda a hannu.
Atletico Madrid dai na tunkarar kofin na 11 ne a tarihi, kuma nasarar ta ta za ta tabbata ne idan har ta yi nasarar wasanninta biyu da suka rage.
Wasa na gaba da ke tunkaro kungiyar shi ne karawarta da Ossasuna a Lahadi 16 ga watan Mayun da muke sai kuma karawarta da Real Valladolid a ranar 18 ga wata
A wani labarin na daban kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, ta sanar da sallamar dan wasanta na gaba Diego Costa yau Talata watanni 6 gabani karewar kwantiraginsa, ba tare da bayyana dalilan da suka haddasa hakan ba.
Sanarwar da Club din ya wallafa a shafinsa ta bayyana cewa Costa da kungiyar sun cimma jituwar kawo karshen kwantiragin a yau, wanda a ka’ida zai kare a ranar 30 ga watan Yunin 2021.
Costa haifaffen dan Brazil mai shekaru 32 da ke takawa Spain leda ya amince da raba gari da Club din ne kan wasu dalilai na radin kai wanda bangarorin biyu basu bayyana ba.
Costa wanda ya fara taka leda da Atletico Madrid tun yana da shekaru 17 a Duniya, ya buga mata wasanni 215 daga 2010 zuwa 2015 da kuma 2018 zuwa 2020 bayan shafe kakar wasa 3 a Chelsea, inda ya zura kwallaye 83 ya kuma taimaka aka zura wasu 36.
Yayin zamansa a Atletico Madrid Costa ya dagewa Club din kofin La Liga 1 a kakar wasa ta 2013 zuwa 2014 sai kuma kofin Cope del Rey a 2013 kana Europa a 2018 sannan UEFA Super Cup 2 a shekarun 2010 da 2018.
Akwai dai masu ganin Costa wanda a yanzu kowanne Club zai iya saya ba tare da biyan kudin sallamar tsohuwar kungiyarsa ba, akwai yiwuwar ya koma taka leda a Firimiyar Ingila