Kasar Senigal Ta Lashe Gasar Kofin Africa A karon Farko Bayan Da ta Doke Kasar Masar.
Kasar Senegal ta lashe gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta Africa Afcon ta shekarar 2021 a wasan karshe wato final da aka buga tsakaninta da kasar masar a filin wasa na Olombe dake birnin Yaounde na kasar kamaru
An shafe mintuna 120 ana fafatawa ba tare da an samu wanda ya ci a fili ba, har sai da aka kai bugun daga kai sai mai tsaron gida, A nan ne Senegal ta doke Masar da ci 4 da 2.
An fara gasar ne da ƙungiyoyi 24, kafin a gangaro zuwa ƙasashe biyu da suka buga wasan ƙarshen a yanzu. Masar ta rasa damarta ta ɗaukar kofin karo na 8, inda ita kuma Senegal ta ɗauki kofin a karon farko
Tun a zagayen farko Sadio Mane, wanda aka zuba wa ido a kansa a ɓangaren ƴan wasan Liverpool ya kasa cin bugun daga kai sai mai tsaron gida da ƙasarsa ta samu, wani abu da ya rage ƙarin guiwar ƴan wasan da farko.