Har yanzu Harry Kane yana fatan zai jagoranci tawagar Ingila a gasar Euro 2028.
Dan wasan na Bayern Munich zai kai kusan shekaru 35 yayin da za a buga gasar a shekarar 2028 amma duk da haka yana sa ran zai ci gaba da zura kwallo a raga a wannan lokaci.
Kane kuma yana neman yin irin abin da Lionel Messi da Cristiano Ronaldo suka yi don samun kwarin guiwa yayin da yake neman ci gaba da taka leda domin yanzu haka yanada shekaru 30 da haihuwa.
“Ina fatan har zuwa wannan lokacin ina cikin ganiyata duk da cewar akwai shekaru biyar kafin lokacin, amma ni dan wasa ne mai jajircewa akan abin da yake nema,” in ji shi.
A wani labarin na daban tsohon dan wasan gaban Manchester United, Wayne Rooney ya samu sabon aikin horarwa bayan barin D C United a satin da ya gabata.
Birmingham City ta sanar da nadin Wayne Rooney a matsayin sabon kocin kungiyar.
Shahararren dan wasan na Ingila da Manchester United, Rooney ya maye gurbin John Eustace a St Andrews bayan ya bar DC United ta kasar Amurka a makon jiya.
Rooney, wanda ya kasance kocin Derby County tsakanin Nuwamba 2020 zuwa Yuni 2022, zai kasance tare da tsoffin abokan wasansa Ashley Cole da John O’Shea a matsayin wani bangare na mataimakansa.
Source LEADERSHIPHAUSA