Juventus zasu fafata da inter milan, sa’annan Inter Milan a karkashin jagorancin mai horarwa, Antonio Conte sun samu nasarar lashe gasar Seria A, sai dai gwagwarmayar wadanda za su samu zuwa gasar Zakarun Turai a kaka mai zuwa ta yi zafi.
Maki 3 ne kawai ya raba Atlanta da ke matsayi na 2 da Juventus da ken a 5 da kwanten wasanni 2.
Atalanta da AC Milan na da maki 75 kowanne, sai Napoli da ke matsayi na 4 na biye da maki 73, sai Juventus da maki 72 a matsayi na 5.
Ana iya fayyace wadanda za su samu shiga gasar zakarun Turai na badi a karshen wannan makon.
Idan Atalanta da Milan suka samu nasara, dukkanninsu za sus amu tikitin shiga gasar, saboda su na gaban Juventus a gwabzawar da suka yi a tsakaninsu.
Wasanni 4 ne kawai Juventus suka samu nasara daga cikin 9 da suka buga a baya bayan nan, kuma su na bukatar doke Inter don samun tikitin gasar zakarun Turai.
Idan Juventus suka gaza doke Napoli don samun ilahirin maki 3, zai zame musu dole su koma fafatawa a gasar Europa a kaka mai zuwa.
‘Yanzu Koch Andrea Pirlo zai yi fatan dan wasan da ke kan gaba a cin kwallaye a gasar Seria A, wato Cristiano Ronaldo ya taimaka wa tawagar wajen samun nasarar da ake bukata.
A wani labarin mai kama da wannan jiya Laraba an buga wasani tsakanin kungiyoyi na yankin Turai, wanda bayan haka ,wasu daga cikin kungiyoyi kama da Juventus suka yi bankwana da gasar ga baki daya.
Da jimawa dai dan wasan kungiyar Christiano Ronaldo na daga cikin yan wasan dake ci gaba da fuskantar suka ko caccaka daga magabatan kungiyar ta Juventus dake yi masa kalon mutumin da ya gaza wajen ceto wannan kungiya tun bayan sayo sa daga Real Madrid.
Yanzu haka kalo ya koma bangaren magabatan kungiyar da shi dan wasan don sanar da matsayar su na ci gaba da taka leda da wannan kungiyar ta Juventus ko raba gari da kungiyar ga baki daya.