Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, hukumar wasannin Judo ta duniya ta dauki matakin haramta wa dan wasan Judo na Aljeriya Fathi Nurain yin wasa har tsawon shekaru 10 saboda kin yin wasa da bayahuden Isra’ilaa wasannin motsa jiki na Tokyo 2020.
Rahoton ya ce wannan mataki da hukumar ta dauka ya shafi har da mai horar da dan wasan na Aljeriya Ammar Bin Yakhluf, wanda ya goyi bayan dan wasan.
Dan wasan an Aljeriya ya ce ya dauki wannan matakin ne na kin yin wasa da bayahuden Isra’ila, saboda nuna adawarsa da zaluncin da Isra’ila take yi kan al’ummar Falastinu.
Ya ce bai yi nadama kan matakin da ya dauka ba, domin kuwa ya san cewa abin ya yi saboda Allah ne ya yi, domin nuna goyon bayansa ga gaskiya da kuma kare akidarsa.
A wani labarin na daban jaridar Leadeship ta Najeriya ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da bankin musulunci na Jaiz ya bayar, ya sheda cewa, Bankin raya ayyukan ci gaba na musulunci ya saka hannun jari na dala miliyan ashirin da biyar a cikin bankin na Jaiz da ke Najeriya.
Ayman Sejiny babban daraktan gudanarwa na bankin raya ayyukan ci gaba na musulunci ya bayyana cewa, sun saka wadannan kudade a Najeriya da nufin ganin an yi amfani da su wajen bunkasa kananan sana’oi da suka durkushe, ko kuma suka samu koma baya, sakamako bullar cutar corona.
Ya ce bankin yana gudanar da ayyukansa ne a Najeriya bisa yarjejeniyoyin da aka rattaba hannu a kansu tare da gwamnatin kasar da kuma sauran bangarori da suke mu’amala da wannan banki, musamman bankin Jaiz, wanda shi ne bankin musulunci a Najeriya.
Tun a cikin shekara ta 2003 ne dai aka kafa bankin Jaiz a Najeriya wanda yake gudanar da ayyukansa bisa ka’idoji na shari’ar musulunci, da suka hada da rashin yin ta’amulli da riba, da kuma kaucewa harkokin kasuwanci da suka shafi abubuwa da aka haramta a muslunci, kamar kasuwancin giya ko abin da ya yi kama da hakan.