Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta bayar da umarnin rufe duk wani gidan gala da ake da shi a jihar.
Shugaban hukumar Abba El Mustapha ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
“A shirye-shiryen ta na shigowar watan Azumin Ramadana, Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab’i ta jihar Kano ta bayar da umarnin kulle dukkannin gidajen Galar da ke fadin jihar Kano,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Hukumar ta ce ba ta ɗauki wannan mataki ba sai da ta zauna ta tattauna da jagororin musu gidajen galar da ke jihar.
Hukumar Tace Fina Finai ta ce dokar za ta fara aiki ne tun daga yau Lahadi har zuwa 1 ga watan Shawwal wato ranar bikin Ƙaramar Sallah.
A sanarwar, Abba El-mustapha ya gargadi masu gidajen wasannin na gala da su guji karya doka inda ya ce duk wanda hukumar ta samu da laifin karya wannan dokar to hakika za ta dauki mataki mai tsauri a kansa wanda ka iya sawa ya rasa lasisin sa na din-din-din.
A wani labarin na daban harin da wasu ƴan bindiga suka kai a ƙauyen Gidan Bakuso na ƙaramar hukumar Gada a jihar Sokoto da ke arewacin Nijeriya, inda sace ɗalibai 15 na wata tsangaya ranar Asabar ya sake jefa yankin cikin zulumi gabanin soma azumin watan Ramadan.
Ƴan bindigar sun kai harin ne a daidai lokacin da gwamnatin ta jihar Sokoto ta ƙaddamar da rundunar tsaro ta ƴan sa-kai a yunƙurinta na shawo kan rashin tsaro da ya addabi jihar.
Kuma hakan na faruwa ne kwana guda bayan wasu ƴan bindiga sun kai hari kan ɗaruruwan Musulmai a yayin da suke sallar Juma’a a Anguwar Makera da ke yankin Kwasakwasa a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna inda suka kashe wasu mutane sannan suka yi garkuwa da wasu.
Kazalika, a dai jihar ta Kaduna, a ranar Alhamis ɗin da ta gabata wasu ƴan bindiga sun kai hari a makarantar firamare da sakandare da ke ƙauyen Kuriga a ƙaramar hukumar Chikun, inda a can ma suka sace ɗalibai da malamansu kusan 300.
Kwana guda kafin harin na Kaduna, wasu ƴan bindiga sun sace fiye da mutum 200, galibinsu mata da ƙananan yara ƴan gudun hijira a Gamboru Ngala a jihar Borno yayin da suka je daji domin saro itacen girki.
Ɗanyen-aiki
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu da gwamnonin jihohin da lamarin ya faru sun sha alwashin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su tare da ƙara ƙaimi wurin tabbatar da tsaro a yankin.
DUBA NAN: Ministan Ilimi Ya Soke Korar Da Jami’a Tayi Ma Wani Dalibi
A saƙon da ya fitar ranar Juma’a, shugaban ƙasar ya ce ya bai wa jami’an tsaron ƙasar umarni su “gaggauta” kuɓutar da mutanen da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a jihohin Borno da Kaduna da ke arewacin ƙasar.