Tsohon dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Fernando Heirro, ya kalubalanci matakin da kociyan tawagar kasar Sipaniya ya dauka na kin gayyatar dan wasan baya na Real Madrid, Sergio Ramos domin bugawa kasar wasannin European Cup da za’a fara nan gaba kadan.
Sergio Ramos ba zai buga wa tawagar wallon kafar Sifaniya gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana ba, sakamakon raunin da ya yi faman jinya a kakar wasa ta shekarar 2020 zuwa 2021 a cewar kociyan tawagar, Luis Enrikue.
Mai koyarwa, Luis Enrikue ya gayyaci Aymeric Laporte mai tsaron baya maimakon Ramos, wanda a cikin watan nan ya zabi komawa buga wa tawagar kasar Sifaniya wasa maimakon Faransa.
Ramos yana cikin ‘yan wasan tawagar Sifaniya da suka lashe manyan kofi uku tsakanin shekarar 2008 zuwa 2012 tun daga lokacin ya zama kashin baya a Sifaniya da Real Madrid baki daya.
A kakar bana ne Ramos ya doke tarihin da mai tsaron ragar Italiya keda shi na yawan buga wa tawagar kwallon kafar Italiya wasa 177 wanda hakan yasa yanzu shine yake da wannan tarihin.
An nada Ramos mai shekara 35 kyaftin din Sifaniya karkashin Luis Enrikue cikin watan Maris a wasan neman shiga gasar kofin duniya da Girka da kuma Kosobo, wanda ya yi rauni ya koma Real Madrid jinya.
Wasanni 21 kacal Ramos ya buga a kakar bana a dukkan fafatawa, bayan da bai yi karawa 31 ba, kuma Enrikue bai gayyaci dan wasan Real Madrid ko daya tawagar Sifaniya ba wanda wannan shine karo na farko da hakan ta faru.
Tun a kakar wasa ta shekarar 2020 ya kamata a buga gasar cin kofin nahiyar Turai, amma cutar koron ta kai tsaikon da aka dage wasannin zuwa watan Yuni da za’a karkare a Yulin shekara ta 2021.
‘Yan wasan da aka gayyata tawagar Sifaniya domin buga gasar nahiyar Turai ta bana:
Unai Simon (Athletic Bilbo) da Dabid De Gea (Manchester United) da Robert Sanchez (Brighton and Hobe Albion) da Jose Gaya (balencia) da Jordi Alba (Barcelona) da Pau Torres (billarreal) da Aymeric Laporte (Manchester City) da Eric Garcia (Manchester City) da Diego Llorente (Leeds United) da Cesar Azpilicueta (Chelsea) da Marcos Llorente (Atletico Madrid) da kuma Sergio Buskuest (Barcelona).
Sauran sun hada da Rodri (Manchester City) da Pedri (Barcelona) da Thiago Alcantara (Liberpool) da Koke (Atletico Madrid) da Fabian Ruiz (Napoli) da Dani Olmo (RB Leipzig) da Mikel Oyarzabal (Real Sociedad) da Albaro Morata (Jubentus) da Gerard Moreno (billarreal) da Ferran Torres (Manchester City) da Adama Traore (Wolbes) da kuma Pablo Sarabia (Paris Saint-Germain).
Heirro Heirro