Jarumar Fina-finan Hausa ta Kannywood, Hadiza Muhammad wadda akafi sani da Hadizan Saima ta bayyana dalilin da yasa bata wasa da cin abinci a duk lokacin da take tsaka da daukar shirin fim.
Hadiza yayin da take amsa tambayoyi a wata hira da tayi da Ibrahim Mandawari a cikin shirinsa na Mushakata, ta bayyana cewa, “a duk lokacin da take tsaka da daukar fim takan yi kokarin samun abinda ta saka a bakin salati saboda abinci shine rayuwa.”
Mai gabatar da shirin na Mushakata, Ibrahim Mandawari ya tambayi Hadizan Saima wani abu da yace masoyanta zasu so sani akan maganar da ake yadawa na cewa, idan zata hakura da komai ba zata hakura da abinci yayin daukar fim ba.?
Sai ta amsa da cewa, Eh! hakane gaskiya bana wasa da cin abinci yayin daukar kowane irin shiri saboda ko babu komai akwai yiwuwar kamuwa da cutar gyambon ciki ga duk wani mutum da yake wasa da cin abinci.
A wani labarin na daban rundunar ‘yansandan jihar Kano ta kama wani matashi dan shekara 25 mai suna Abba Garba Ibrahim da laifin kashe abokinsa mai suna Zaharaddeen Iliyasu mai shekaru 22 har lahira.
Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 29 ga Maris, 2024, a Chiranci Dorayi kwatas a Kano.
Kamar yadda wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan (PPRO) jihar ya fitar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, inda ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce, an kira jami’ansu cewa, rikici ya barke tsakanin wasu abokanai biyu, hakan ya jawo daya ya buga wa daya wuka.
“Da isar jami’anmu, tuni an garzaya da gawar zuwa asibitin kwararru na Murtala Mohammed Kano, inda wani likita ya tabbatar da mutuwarsa nan take.”
An dai cafke wanda ake zargin ne, Abba Garba Ibrahim a hanyarsa ta tserewa zuwa Jamhuriyar Nijar.
Duba Nan: Tinubu Zai Halarci Rantsar Da Shugaban Kasar Senegal
“An mika wanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na rundunar ‘yansanda, sashen kisan kai domin gudanar da cikakken bincike,” inji shi.