Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Erling Braudt Haaland ba zai sami damar buga wasan da Manchester City zata ziyarci Brighton a wasan mako na 29 da ya zama kwantai a watan jiya.
Kocin kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Joseph Guardiola ne ya bayyana haka ga manema labarai yayin daukar atisayen kungiyar gabanin wasan da zasu fafata a yau Alhamis a filin wasa na American Express Stadium da ke Brighton.
Haaland ya zama zakaran gwajin dafi a wasannin gasar Firimiya inda yanzu haka ya jefa kwallaye 20 a gasar, shine ya lashe kyautar takalmin zinare a kakar wasan da ta gabata da kwallaye 36.
City na fatan ganin ta doke Brighton a wasan yau domin matsowa kusa da masu jan ragamar gasar Firimiya Arsenal wadda ta yi wa Chelsea kaca kaca a makon jiyaKocin kungiyar kwallon kafa ta Aston Villa da ke Ingila, Unai Emery ya sabunta yarjejeniyar zamansa a kungiyar har zuwa shekarar 2027.
Emery, ya karbi ragamar jagorancin kungiyar a watan Nuwamban 2022 lokacin da kungiyar ke matsayin na 17 a teburin Firimiyar Ingila.
Aston Villa ta yaba da yadda kocin mai shekaru 52 ya sauya kungiyar cikin kankanin lokacin, inda yanzu ta ke a matsayi na hudu a gasar.
Idan kungiyar ta karkare a matsayin da ta ke, hakan zai ba ta damar buga gasar zakarun Turai a kaka mai zuwa.
Duba Nan: Tunde Onakoya Dan Wasan Chess Dake Kokarin Nemawa Najeriya Suna
Unai Emery, ya horas da kungiyoyi irin su Sevilla, Villarreal, Arsenal, PSG da sauransu kafin zama kocin Aston Villa.