Gwamnatin Najeriya za ta gana da ƙungiyar ƙwadago ta NLC kan tallafin mai
Ana sa ran wakilan gwamnatin Najeriya za su gana da shugabannin kungiyar kwadago ta kasar ta NLC a yau Laraba da karfe biyu na rana a kan shirin gwamnati na janye tallafin mai.
Shugaban kungiyar ta NLC, Joe Ajaero, shi ne ya bayyana haka a wata hira da tashar talabijin ta Channels ta yi da shi a yau Laraba.
Mista Ajaero ya ce tun da farko kamata ya yi a ce Shugaba Tinubu ya nemi sanin illa ko abin da zai iya biyo bayan cire tallafin ga talakawa ƴan Najeriya kafin ya furta magana a kai.
Ya ce matsayin NLC a bayyane yake cewa idan har shugaban yana da kyakkyawar niyya da nufi a game da lamarin to kamata ya yi a ce an samar da wata madogara da ƴan kasar za su karkata ga ita idan aka cire tallafin.
Shugaban na NLC ya bayyana wasu daga cikin abubuwan da ya ce kamata ya yi gwamnati ta yi kafin ta ambaci batun cire tallafin, abubuwan sun hada da gyara matatun kasar hudu samar da kyakkyawan tsarin sufuri ga ma’aikata da sauran tanade-tanade.
Furucin da Bola Tinubu ya yi a jawabinsa na farko bayan rantsuwar kama aiki ranar Litinin cewa babu sauran tallafin mai, ana ganin shi ne ya janyo jama’a suka shiga tururuwar sayen mai yayin da masu gidajen mai suka kara kudi,lamarin da ya haddasa dogayen layukan sayen mai a kasar.
A jawabin Shugaba Tinubun ya nuna cewa kasafin kudin da ya gada babu tallafin man, kuma kamar yadda gwamnatin da ya gada ta tsara daga watan Yuni babu sauran maganar tallafi.