Kasar Guinea ta doke abokiyar karawarta Equatorial Guinea a wasan da suka fafata na zagaye na 16 a gasar cin kofin Afirika da ake bugawa a kasar Cote de’Voire.
Mohamed Bayo ne ya ci kwallo a minti na 98 a gasar cin kofin Afrika ta 2023,wanda yasa Guinea ta kai zagayen kusa da na kusa da na karshe, bayan da ta doke Equatorial Guinea da ci 1-0 a daren Lahadi.
Da wannan ne yasa kasar ta Guinea zata hadu da kasar Dimokuradiyyar Congo wadda ta doke kasar Masar da ci 8-7 a bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan tashi canjaras a wasan da suka buga.
A wani labarin na daban kocin Fc Barcelona Xavi Hernandez ya bayyana aniyarsa na aje aikin horar da kungiyar a karshen kakar wasanni da ake bugawa ta bana.
Xavi wanda tsohon dan wasan tsakiyar Barcelona ne inda ya shafe shekaru da dama a matsayin dan wasa,ya bayyana haka ne bayan rashin nasarar da kungiyar tayi a hannun Villareal da ci 5-2 a ranar Asabar.
Na tabbata cewa Barcelona gida ne a wajena kuma sun nuna mani kauna a kowane lokaci da na sami kaina a matsayin dan wasa kokuma koci,amma wannan lokaci ne da ya kamata in ajiye wannan aiki inji Xavi.
Tun bayan zuwan Xavi Barcelona ya lashe kofin Laliga 1 da kuka Spanish Super Cup,amma kungiyar na fuskantar kalubale a wasanninta na bana.
Source: LEADERSHIPHAUSA