Kocin Manchester City, Pep Guardiola ya ce ba zai yiwu ‘yan wasansa su dora alhakin gaza lashe wasaninsu na baya -bayan nan kan rashin sa’a ba, bayan da ssuka buga kunnen doki da Crystal Palace a ranar Asabar.
Manchester City na kan gaba a wasan da ci 2 babu ko daya har zuwa lokacin da ya rage saura minti 15 a tashi wasan, amma ‘yan wasan Palace, Jean-Philippe Mateta Michael Olise suka farke kwallayen.
Wannan ne karo na hudu a cikin wasanni shida da Manchester City ke yin canjaras bayan sun shiga gaba a wasan, lamarin da ya sa yaannzu Liverpool ke gabansu da maki uku, kuma suna da kwanten wasa guda daya.
Guardiola ya ce lallai ba rashin sa’a ba ce, sakamakon ya dace da irin kokarin da ‘yan wasansa suka yi.
Manchester City, wadanda suka yi wannan wasa ba tare da dan wasan gabansu, Erling Halaand ba, sun kai harin cin kwallaye har sau 19, idan aka kwatanta da na takwarorinsu, wadanda suka kai 5.
A wani labarin na daban hukumar Kididdiga Ta Kasa (NBS), ta ce farashin kayayyaki sun kara hauhawa, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, kuma rabon da a ga hakan tun a shekarar 1996.
Nijeriya dai na fuskantar hauhawar farashin kayan masarufi da sauran nau’ikan kayayyakin amfanin yau da kullum.
A rahoton da ta fitar NBS, ta ce an samu karin hauhawar farashin kayayyaki a watan Nuwamba da kashi 0.87 cikin 100, idan aka kwatanta da watan Oktoban da ya gabata.
Hauhawar farashin kaya a Nijeriya yanzu ya haura kashi 27.33 cikin 100 zuwa kashi 28.20 ciki 100, kuma rabon da a shiga irin wannan yanayi na tashin farashin kayayyaki tun 1996.
Source: LEADERSHIPHAUSA