Gasar cin kofin kwallon kafa na duniya ta zo karshe a yau Lahadi inda za a kara tsakanin kasashen Argentina da Faransa a birnin Doha dake kasar Qatar.
Jimillar kudin da za a fitar na kyautuka ga kasashen da suka nuna kwazo har suka halarci gasar ya kai $440 miliyan.
Kasashen da suka fara samun kyauta daga cikin kudin sun hada da wadanda aka fitar tun daga matakin farko har zuwa wacce a yau zata yi nasarar lashe gasar tare da daukar kofin.
Makuden kudin da za a bada kyauta na kungiyoyin da suka kasance zakaru a gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya da ake yi a Qatar a 2022 ta kai $440 miliyan.
Gasaar da ake yi a 2022 ta samu kungiyoyi 32 daga kasashe daban-daban na duniya.
Kungiyoyin da suka fice daga gasar tun a matakin farko sun hada da Qatar, Ecuador, Wales, Iran, Mexico, Saudi Arabia, Denmark, Tunisia, Canada, Belgium, Germany, Costa Rica, Serbia, Cameroon, Ghana, Uruguay kuma kowannensu zasu samu $9 miliyan.
Kungiyoyin da suka je zagayen kasashe 16 sun hada da USA, Senegal, Australia, Poland, Spain, Japan, Switzerland, Korea ta Kudu kuma dukkansu zasu samu $13 miliyan.
Wadanda suka kai ga kwata final sun hada da Brazil, Netherlands, Portugal da Ingila kuma zasu samu $17 miliyan kowannensu.
Kasar da ta kasance ta hudu ita ce Morocco, zata samu $25 miliyan.
Wacce ta dauka na uku ita ce Croata ta zamu $27 miliyan.
Kasar da ta kasance ta biyu tsakanin Argentina ko Faransa za ta tafi gida da $30 miliyan yayin da wanda yayi nasarar lashe gasar zai samu $42 miliyan.
Wannan yawan kudin ya karu daga $40 miliyan na gasar 2018. Kafin 2016, kungiyoyin da suka yi nasarar lashe gasaar kwallon kafa ta duniya bata samun $10 miliyan.
A 2002, an dinga matsantawa FIFA da ta kara yawan kudin kyautar gasar. Gasar zata zo karshe a ranar Lahadi, 18 ga watan Disamban 2022.
Najeriya bata smau halarta ba Tun farko dai kasar Najeriya bata samu halarta ba saboda lallasa ta da aka yi tun a lokacin fitar da kasashen da zasu halarci Gasar.