Gakpo ya yi saurin komawa Liverpool – Koeman
Kociyan Netherlands, Ronald Koeman ya ce Cody Gakpo ya yi saurin komawa Liverpool ya kasa taka rawa a kungiyar da ke fuskantar kalubale a bana.
Mai shekara 23 ya taka rawar gani a gasar kofin duniya a Qatar da cin kwallo uku a wasa biyar, bayan da Netherlands ta kai quarter-finals.
Sai dai ya kasa cin kwallo a wasa shida a Liverpool, tun bayan da ya koma Anfield da taka leda daga PSV Eindhoven a watan Janairu.
”Ya koma kungiyar da ba ta yin kokari a kakar nan,” in ji Koeman.
”Abu ne mai dan karen wahala a makomar dan wasa matashi da baya cin kwallo, kuma kungiya ba ta cin wasanni, sannan ba a ganin mahimmanci ka.”
”Idan dan wasa ne da ya kai shekara 28 mai dinbin kwarewa, abin zai zama na daban.”
Koeman tsohon kociyan Everton, wanda ke jan ragamar Netherlands karo na biyu ya ce matashin dan wasan Netherlands kan fuskanci kalubale idan ya koma fitatciyar kungiya.
”Akwai wasu matasan Netherland da dama da suka koma babbar kungiya amma suka kasa taka rawar gani ciki har da Ryan Gravenberc, wanda baya buga wasa a Bayern Munich.
Kafin Gakpo ya koma Liverpool ya ci kwallo tara ya bayar da 12 aka zura a raga a wasa 14 a PSV a kakar bana a babbar gasar tamaula ta Netherlands.
Liverpool, wadda aka fitar da ita daga Carabao da FA Cup a bana tana ta 10 a teburin Premier League da maki 29, za ka kara da Real Madrid a Champions League.