Gasar Firimiya ta Ingila tana daya daga cikin manyan gasanni masu daraja a duniya kuma kawo yanzu masu koyarwa 12 aka kora a Premier League ta bana, wadda saura wasanni tara-tara a kammala wasanni.
A ranar Lahadi 2 ga watan Afirilu, kungiyar kwallon kafa ta Leicester City, wadda a baya ta taba daukar gasar ta Ingila ta sanar da korar Brendan Rodgers, a matsayin kociyan ta sannan da yamma Chelsea ta sanar ta sallami Graham Potter ita ma.
Scott Parker, Bournemouth, Kungiyar kwallon kafa ta Bournemouth ce ta fara korar Scot Parker ranar 30 ga watan Agustan shekarar da ta wuce, bayan da Liberpool ta doke su da ci 9-0 a gasar Premier League.
Sabuwar kungiyar da ta hau Premier daga Championship, wadda Parker ya sa ran za’a fitar da kudi domin sayo karin sababbin ‘yan kwallo, amma hakan bai yi wu ba inda aka nada Gary, O’Neil ne ya maye gurbinsa na wucin gadi.
Thomas Tuchel, Chelsea
Sai Chelsea, bayan da mai koyarwa Thomas Tuchel ya ja ragamar kungiyar ta lashe UEFA Champions League a kakar wasa ta 2020 zuwa 2021 da UEFA Super Cup da FIFA Club World Cup a kakar, Chelsea ta sallami Tuchel ranar 7 ga watan Satumba.
An kuma sallame shi bayan da kungiyar ta yi rashin nasara da ci 1-0 a hannun Dinamo Zagreb a Champions League amma tun kafin a fara kakar Chelsea ta kashe kudi fam miliyan 310m wajen sayo sabbin ‘yan kwallo, amma sai kungiyar ba ta taka rawar gani.
Bruno Lage
Wolberhampton Wanderers, Sannan a ranar 2 ga watan Oktoba, kungiyar kwallon kafa ta Wolberhampton ta kori Bruno Lage, bayan rashin nasara da ci 2-0 a gidan kungiyar kwallon kafa ta West Ham United.
Tun farko Wolbes ta sa kanta cikin kungiyoyin da za’a yi tata burza da ita a jerin ‘yan goman farko, ashe ba haka batun yake ba da ta kai ta raba gari da kociyan sannan daga baya ta nada Julen Lopetegui tsohon kociyan Sebilla da Real Madrid, wanda ya maye gurbin Lage.
Steven Gerrard
Aston Billa Ita ma kungiyar kwallon kafa ta Aston Billa ta sa ran a kakar nan za ta iya samun gurbin gasar zakarun Turai ko a Europa ko kuma a Confrence League, bayan da ta fitar da kudi ta sayo sabbin ‘yan wasa.
Sai dai Gerrard ya tafka kuskure da ya canja kyaftin din kungiyar, sannan ‘yan wasa irin su Philippe Coutinho, Emiliano Buendia, Boubacar Kamara, Jacob Ramsey da Leon Bailey sun kasa nuna kwarewarsu a Premier
League wanda hakan yasa aka kore shi aka nada tsohon kociyan Arsenal, Unai Emery.
Ralph Hasenhüttl
Southampton Southampton ta kori Hasenhüttl ranar 6 ga watan Nuwamba ta kuma nada Nathan Jones ya maye gurbinsa amma idan ba’a manta ba Hasenhüttl ya fara aiki da kungiyar a shekarar 2018, amma ba ta haura mataki na 11 a teburin Premier har zuwa kakar 2019 zuwa 2020 kenan ba ci gaba.
An sallame shi a lokacin da ya kai kungiyar cikin ‘yan ukun karshe da yin nasara uku da canjaras uku aka doke shi wasa takwas hakan ya sa shugabannin kungiyar suka yanke shawarar sallamarsa.
Frank Lampard, Everton
Daga kungiyar Eberton kuwa da aka fara kakar bana Eberton ta fara da taka rawar gani daga baya komai ya koma baya a kungiyar ta kasa yin abin kirki kuma kungiyar kan kasa zura kwallo a raga, sannan ba ta buga wasa mai ban sha’awa da sauran matsaloli.
Bayan wasanni 20 a Premier League, Eberton ta ci karawa uku da canjaras shida da rashin nasara 11 hakan ya kai kungiyar ta 19 a kasan teburi kuma aka maye gurbinsa da Sean Dyche.
Jesse Marsch
Leeds Leeds United ta kori Marsch, bayan da ta yi rashin nasara a hannun Nottingham Forest 1-0, washe gari ta sanar da korar dan kasar Amurkan duk da ya hada maki 18 ya ci wasa hudu da canjaras shida aka doke shi sau 10, hakan ya sa kungiyar ta koma cikin ‘yan kasan teburi kuma daga baya ta nada Jabi Gracia a matakin sabon kociyanta ranar 21 ga watan Fabrairu.
Nathan Jones
Southampton Karo na biyu da Southampton ta kori koci a kakar nan – an sallami Jones,
bayan da wasu fitattun ‘yan wasan kungiyar suka yi korafi a kansa kuma aka kore shi bayan da Southampton ta yi rashin nasara a hannun Wolbes da ci 2-1 duk da cewar ita ta fara cin kwallo, sannan Wolbes ta karasa wasan da ‘yan wasa 10 a cikin fili.
Patrick Vieira
Crystal Palace Kungiyar Crystal Palace ta dora a wasanninta, bayan da ta sallami Bieira, kwana biyu tsakani kafin ta buga wasan da kungiyar Arsenal ta yi nasara a kanta da ci 4-1 a Emirates a wasan hamayya.
Sai dai tun kafin wasan, Crystal Palace ta kasa cin wasa a shekarar 2023, wadda ta nada Paddy McCarthy na rikon kwarya kuma rashin kokarin kungiyar a 2023 ya sa ta fada wani hali na fuskantar nutsewa nan da nan ta kara bai wa Roy Hodgson aikin jan ragamar kungiyar.
Antonio Conte,
Tottenham Conte da Tottenham sun raba gari bayan da ya caccaki ‘yan wasa da kungiyar, bayan sun tashi wasa 3-3 da kungiyar kwallon kafa ta Southampton a gasar Premier Leage ta Ingila.
Tottenham ta fara kakar wasa ta bana da kafar hagu cikin ‘yan hudun farko, daga baya aka yi waje da Champions League da FA Cup ba ita ta dauki Carabao Cup na bana ba sannan kungiyar wadda yanzu take ta biyar a teburi ta yi shekara 15 ba tare da daukar babban kofi ba kawo yanzu ta nada Cristian Stellini zuwa karshen kakar bana.
Brendan Rodgers, Leicester City
Leicester City ta kori Brendan Rodgers bayan da Crystal Palace ta doke ta 2-1 a gasar Premier League ranar Asabar kuma wasa na biyar da aka doke kungiyar a filin was ana King Power daga shida da ta kara a bayan nan da hakan ya sa ta koma cikin ‘yan karshen teburi.
Leicester City ta dauki Rodgers aiki a watan Fabrairun shekara ta 2019, wanda ya lashe FA Cup a kungiyar a shekarar 2021 kuma a yanzu za’a iya cewa daga kungiyoyi tara da ke kasan karshe kungiyoyin West Ham United da Nottingham Forest ne kadai ba su sallami masu horar da su ba.
Graham Potter, Chelsea
Chelsea ta sallami Graham Potter, bayan wata bakwai yana jan ragamar kungiyar sai dai ranar Asabar din data wuce ne Aston Billa ta doke.
Chelsea da ci 2-0 a wasan mako na 29 na Gasar Premier.
Wasa na 11 da aka doke Potter a cikin wasanni 31 da ya yi jagoranci tun
bayan maye gurbin Thomas Tuchel a ranar 8 ga watan Satumba sai dai Chelsea, wadda ta kashe sama da fam miliyan 550 wajen sayo sabbin ‘yan wasa, za ta dauki wani kocin a kakar nan. Masu koyarwar da aka kora a Premier League a kakar wasa ta 2022 zuwa 2023.
Scott Parker Bournemouth 30 ga watan Agustan 2022 Thomas Tuchel Chelsea 7 ga watan Satumbar 2022.
Bruno Lage Wolves 2 ga watan Oktoban 2022. Steben Gerrard Aston Billa 20 ga watan Oktoban 2022.
Ralph Hasenhuttl Southampton 7 ga watan Nuwamba Frank Lampard Eberton 23 ga watan Janairun 2023.
Jesse Marsch Leeds 6 ga watan Fabrairun 2023.
Nathan Jones Southampton 12 ga watan Fabrairun 2023 Patrick Bieira Crystal Palace 17 ga watan Maris 2023 Antonio Conte Tottenham 26 ga watan Maris 2023
Brendan Rodgers Leicester 2 ga watan Afirilun 2023.
Graham Potter Chelsea 2 ga watan Afirilun 2023.