Fifa Ta Dakatar Da Hukumomin Wasannain Kwallon Kafa Na Kasashen Kenya Da Zimbabwe.
Matakin na hukumar kwallon kafa ta duniya, ya biyo bayan abinda ta kira tsoma bakin da gwamnatocin kasashen Zimbabwe da Kenya suke yi ne a cikin tafiyar da hukumomin na kasashensu.
A watan Nuwamba na shekarar 2021 ne dai ma’aikatar wasanni ta kasar Kenya ta sanar da dakatar da hukumar wasanni ta kasar,inda ta kafa wani kwamiti na daban wanda zai cigaba da kula da harkokin wasannin kwallon kafa ta kasar.
Hukumar kwallon kafa ta duniya, ta zargi gwamnatin ta Kenya da tsoma baki acikin harkokin wasannin kasar.
A can kasar Zimbabwe ma gwmanatin kasar ta dakatar da hukumar wasannin tare da nada wasu shugabanni na musamman.