Hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta fitar da sunayen alkalan wasan da za su busa gasar Olympics da za a fara a watan Yuli a birnin Paris na Faransa.
Hukumar ta fitar da sunayen alkalan wasa 12 daga kasashen Afrika wadanda za su wakilci nahiyar.
Cikin alkalan da ta fitar da sunayensu babu dan Nijeriya ko daya, duk da cewa kasar tana samun habbakar kwallon kafa.
Irin wannan ce ta faru ga kasar a gasar cin kofin duniya da aka yi a 2022 a Qatar.
A tattaunawar da BBC ta yi da tsohon alkalin wasa da ya kai matakin FIFA, Ibrahim Umar Fagge, kan ko me ke janyowa ana barin Nijeriya a baya.
“Akwai dalilai da dama, na farko shi ne ko da matashi ya samu damar zama alkalin wasan FIFA, ba sa iya samun horon da ya kamata wanda zai kai shi ga fara hura wasanni a matakin manyan gasa kamar kofin duniya.
“Na biyu da yawan alkalan suna da matsala ta rashin lafiya da ba sa iya kai wa ga inda ake so. Akwai kuma matsalar shekaru mafi yawa daga cikin mutanen namu tsofaffi ne.
“Bugun zuciyarsu da yadda jinin ke zagaye a jikinsu akwai hatsari a bar su, su ci gaba da guje-guje.
“Na karshe shi ne a Nijeriya babu na’urar VAR da kw taimaka wa alkalin wasa,” in ji shi.
A dokar FIFA alkalin wasa ba zai busa manyan gasar da ake yi ba sai ya kware wajen amfani da VAR.
DUBA NAN: Kiraye Kirayen Gwamnonin Kano Da Kebbi A Bikin Sallah
Nijeriya dai ta jima tana samun koma baya ta fuskar gayyatar alkalan wasa domin busa wasanni a manyan gasa da ake yi a duniya.