Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta kammala daukar matashin dan wasan tsakiya daga Borrusia Dortmund akan zunuzurutun kudi Yuro miliyan 103
Bellingham wanda ya je Dortmund shekaru uku da suka gabata ya godewa Magoya bayan tsohuwar kungiyar tasa inda yace duk da yana fatan nasara a sabuwar kungiyarsa amma ba zai taba mantawa da kungiyar ta Jamus ba
Real Madrid na neman karfafa yan wasansu bayan tashin da wasu Yan Wasa sukayi da Suka hada da Benzema,Hazard,Asensio da kuma Mariano Diaz
Bellingham wanda ya lashe kyautar gwarzon Dan wasan gasar Bundesliga ta kasar Jamus ya zama Dan wasa na biyu mafi tsada da Real Madrid ta taba saye bayan tsohon kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Belgium Eden Hazard
A wani labarin na daban kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint Germain da ke buga gasar Ligue 1 ta kasar Faransa, na duba yiwuwar sayar da tauraron dan wasanta, Kylian Mbappe a bana domin guje wa rasa shi a badi inda kwantiraginsa zai kare.
Mbappe ya aike wa PSG wakisar cewar ba zai kara rattaba hannu kan wani sabon kwantiragi ba, hakan ya sa kungiyar ke shawarar rabuwa da shi tun yanzu don gujewa rasa shi a kyuata yayin da kwantiraginsa ya kare a karshen kakar badi.
Real Madrid ta nuna sha’awar daukar dan wasan amma ya watsa mata kasa a ido, amma barin kungiyar da Karim Benzema ya yi ka iya kara janyo hankalin kungiyar wajen neman Mbappe.
Kylian Mbappe wanda ya zo PSG a matsayin aro kafin su saye shi daga Monaco a kan kudi Yuro miliyan 180 ya zura kwallaye 212 a wasanni 260 da ya buga, kuma ya jefawa kasarsa Faransa kwallaye 38 a wasanni 68 ciki har da kwallo uku rigis da ya jefa a wasan karshe na gasar kofin duniya da suka buga da kasar Ajantina.
Mbappe ka iya zama shahararren dan wasa na biyu da zai bar kungiyar a bana bayan da Lionel Messi ya yanke shawarar barin kungiyar a bana.