Dan wasan dara na Chess daga kasar Sin Ding Liren, ya doke takwaransa na Rasha Ian Nepomniachtchi, da maki 2.5 da 1.5, yayin wasan karshe na gasar fid da gwani ta bana ta kungiyar wasan dara na duniya(FIDE) da suka buga a jiya Lahadi. Da wannan nasara, Ding ya zamo Basine na farko da ya taba lashe wannan kambi na gasar Chess ta duniya.
Da fari ‘yan wasan biyu sun yi kunne doki da maki 7 da 7, a wasan da suka buga ranar Asabar, inda suka shafe sa’o’i 6 da mintuna 33 suna fafatawa, kana suka sake komawa wasan kammala gasar a jiya Lahadi, kuma bayan fafatawa mai zafi, Ding ya lashe makin karshe a zagaye na 4.
Nasarar da Ding ya samu a wannan karo ta kafa sabon tarihi, kasancewar a yanzu haka kasar Sin din ce ke rike da kambin gasar ajin maza da na mata. (Saminu Alhassan)
Source:LeadershipHausa