De Bruyne yana takarar gwarzon mako na Champions League.
Hukumar kwallon kwallon kafa ta Turai, Uefa ta sanar da ‘yan wasan da ke takarar lashe kyautar gwarzon mako a Champions League.
Cikin ‘yan wasan da ta bayyana har da Kevin De Bryune na Manchester City, wanda ya buga wasan farko a gasar zakarun Turai a Sifaniya ranar Talata.
Real Madrid da Manchester City suka tashi 1-1 a wasan farko na daf da karshe a Champions League a Santiago Bernabeu.
Sauran da ke takara sun hada da dan wasan Real Madrid, Vinicius Junior da ‘yan wasan Inter Milan biyu wato, Henrikh Mkhitaryan da kuma Nicolò Barella.
Real Madrid ce ta fara cin kwallo ranar Talata ta hannun Vinicius Junior, daga baya City ta farke – za su buga wasa na biyu ranar Laraba 17 ga watan Mayu.
Ranar Juma’a za a rufe zaben gwarzon dan kwallon mako a Champions League da za ku iya kada kuri’a a shafin Uefa.
Daya wasan na daf da karshe a Champions League kuwa da aka kara ranar Laraba, Inter Milan ce ta yi nasara da ci 2-0.
Minti takwas da take leda Inter ta fara zura kwallo a raga ta hannun Edin Dzeko, sannan Henrikh Mkhitaryan ya kara na biyu minti uku tsakani.
Ranar Talata 16 ga watan Mayu, Inter Milan za ta karbi bakuncin AC Milan a wasa na biyu a daf d
a karshe a babbar gasar tamaula ta Ingila.