Kungiyar Dambe Warriors wadda ta kudirin aniyar zamanantar da wasan Dambe domin tafiya dai-dai da zamani, wasan Damben na kakar bana an gudanar da wasan karshe a Kano inda matasan ‘yan wasa masu jini a jika daga matakai daban-daban suka fafata kuma aka karkare wasan cikin nasara.
A nasa jawabin, Gwamnan Kano wanda Mai Bai wa Gwamna Shawara Kan harkokin matasa da wasanninl ya wakilta ya nuna gamsuwa bisa yadda kungiyar Dambe Warriors ta dauki sabon salon kyautata wasan Dambe zuwa wani Matsayin da ‘yan Dambe suka fara karbar albashi mai tsoka, sannan kuma ya ce sai a wannan lokaci ne dan Dambe yake karbar makudan kudade ga wanda ya samu nasara.ya ce babu shakka Dambe Warriors sun yi abin a yaba kwarai da gaske.
Shima a nasa jawabin, Mai martaba Sarkin Kano wanda Ci Garin Kano ya wakilta ya bayyana farin cikinsa bisa zabar Kano a matsayin wurin da za’a gudanar da wannan gagarumin wasa, haka kuma Ci garin na Kano ya jinjina wa kungiyar Dambe Warriors bisa wannan kyakkyawan tunani.
Tun da fari, Shugaban Sashen Lura da Wasanin Garganiya na Kasa a jawabin bude wasan ya bayyana cewa, an zabi gudanar da wasan karshen a Kano ne bisa la’akari da kyakkyawan zaman lafiya da kuma kasancewar Jihar Kano jihar da ake alfahari da wasannin gargajiya, kuma Kano gidan wasan Dambe ne.
DUBA NAN: Ministan Ilimi Ya Soke Korar Da Jami’a Tayi Ma Wani Dalibi
Don haka sai ya gode wa kungiyar Dambe Warriors bisa gagarumar gudunmawar da suke bayarwa wajen sake fasalin Dambe a kasarnan.