Da gaske Ronaldo ne matsalar Manchester United?
Rashin tabbacin da Manchester United ke da shi na nasara a duka gasar da take bugawa ta haifar da muhawarar neman wanda shi ne matsalar kungiyar.
Magoya bayan kungiyar a fadin duniya na yawan dora zargin rashin koakarin kungiyar kan Cristiano Ronaldo.
Suna yawan zargin yana tsarata ‘yan wasan irinsu Rashford da Elenga da dai sauransu, suna zargin rashin kokarin Bruno ma na da alaka da zuwan Ronaldo.
To amma wadanda ba su da wannan ra’ayin sun rika mai dawa masu ra’ayin martani a jiya Asabar, bayan nasarar da United ta samu kan Tottenham da ci 3-0 a Old Trafford.
Yanzu Ronaldo na da kwallo 12 a Premier Mo Salah ne kawai ke gaban shi, sai dai wadanda suke kan-kan-kan, ma’ana ya fi kowa yawan cin kwallo a kungiyarsa.
READ MORE : Ka fita daga harkar Gwamna Umahi – APC ta gayawa Gwamna Wike.
Irin kwallon da ya buga a jiya da hazakar da United suka sa a wasan sun kwana biyu ba su sanyata haka ba, babu mamaki hakan na da alaka da neman nasarar gurbi na hudu da suke yi.
“A shekara 37, Ronaldo shi ke jan ragamar United kuma a ce shi ne matsalar kungiyar ba a yi masa adalci ba” in ji wani magoyin bayan United.
Ya kara da cewa yaran da ake bai wa dama a baya me suka yi, babu wanda ya yi abin da Ronaldon yake yi a yanzu.