Golan Real Madrid, Thibaut Courtois, ya samu rauni a gwiwarsa ta hagu, kuma da alama ba zai samu damar buga wasanni mafi yawa a kakar wasa ta bana ba.
Courtois, wanda aka ba shi kyautar Gwarzon mai tsaron gida a duniya a kyautar Ballon d’Or a bara, ya lashe gasar La Liga ta Spain sau biyu tun da ya koma Real a 2018.
Ya buga wa Real wasanni 230, wacce za ta kara da Athletic Bilbao a wasansu na farko na gasar La Liga a ranar Asabar.
Courtois ya lashe gasar Premier sau biyu tare da Chelsea kafin ya koma Real a 2018.
Ya kuma lashe gasar zakarun Turai a 2022, inda ya nuna bajinta a wasan karshe da Liverpool.
A wani labarin na daban kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen ta cimma yarjejeniya da Tottenham wajen sayan dan wasan gaba na kungiyar Harry Kane, a kan kudi €100 kamar yadda jaridar The Athletic ta ruwaito.
Kane Ya Zura Kwallaye 4 A Ragar Shaktar Yayin Da Bayern Ke Cigaba Da Nuna Sha’awar Daukar shi
Tun a watan da ya gabata Tottenham tayi fatali da tayin kudi har sau uku da Bayern Munchen take kaiwa domin siyan dan wasan mai shekara 30 a duniya.
Kane, ya bayyana cewa yana son sanin makomar sa kafin kungiyar ta Tottenham ta buga wasan ta na farko a gasar premier league ta Ingila.
Yanzu Bayern Munchen tana jiran amincewar dan wasa Kane domin ci gaba da kammala cinikin.
Tun bayan da dan wasa Robert Lewandowski ya bar Bayern Munchen ya koma Barcelona kungiyar bata sayi babban dan wasan gaba ba.