Seko Fofana da Jean-Philippe Krasso ne suka zura kwallo a raga wanda ya taimakawa kasar Cote d’Ivoire mai masaukin baki samun nasara akan Guinea-Bissau da ci 2-0, a daren Asabar.
Kasar Cote d’Voire ta samu nasarar ne a wasan farko da ta buga a gasar ta bana a filin wasa na Alassane Outara da ya cika makil da magoya baya.
Cote d’Ivoire, wacce ke neman lashe kofin a karo na uku bayan nasarar da ta samu a shekarun 1992 da 2015, ta mamaye wasan na tsawon Lokacin ba tareda baiwa kasar Guinea Bissau wata dama ba.
A wani labarin na daban masu magoya bayan kungiyar Napoli da ke buga gasar Serie A sun mamaye Abidjan domin mara wa daya daga cikin nasu, tauraron Super Eagles, Victor Osimhen baya.
Wasu magoya bayan Napoli sun isa Abidjan ta kasar Cote d’Ivoire, domin nuna goyon bayansu ga fitaccen dan wasansu, Victor Osimhen gabanin gasar cin kofin nahiyar Afrika ta 2023 (AFCON).
Wasan farko da Nijeriya za ta buga shi ne wanda za su kara da kasar Equatorial Guinea a ranar Lahadi.
Osimhen ne, zai jagoranci ‘yan wasan gaban Super Eagles yayin da Nijeriya ke neman lashe kofin Afirka karo na hudu a filin wasa na Alassane Ouattara.
Dan wasan na Nijeriya mai shekaru 25 ya taka rawar gani a kakar wasanni biyu da suka gabata, inda ya taimaka wa Napoli ta lashe gasar Seria A ta farko cikin shekaru 30.
Source: LEADERSHIPHAUSA