Masu masaukin baki na gasar cin kofin kasashen Afirika Cote de’Voire ta samu nasarar tsallakawa zuwa matakin na kusa da na karshe bayan doke abokiyar karawarta kasar Mali bayan shafe mintuna 120 ana fafatawa.
Mali ce ta fara jefa kwallo ta hannun Nene Dorgeles a minti na 71 da fara wasa,amma Cote de’Voire ta farke ta hannun Simon Adingra a minti na 90.
Hakan yasa alkalin wasa Muhammad Adel ya kara mintuna 30 domin cigaba da fafatawa,a minti na 30 na mintunan da aka kara Oumar Diakate ya jefa kwallon da ta zama sanadiyar tsallakawar Cote de’Voire zuwa matakin na kusa da na karshe.
A wani labarin na daban hukumar da ke shirya gasar cin kofin kasashen Afirika na AFCON (CAF) ta bayyana adadin makudan kudaden da kasar da ta lashe kofin AFCON na bana zata samu.
CAF ta bayyana cewar duk kasar da ta yi nasara a gasar AFCON ta 2023 za ta samu makudan kudi har dala miliyan 7,yayinda kasar da tazo a matsayi na biyu zata karbi dala miliyan 4.
Haka kuma kasashen da suka buga matakin na kusa da na karshe kowace zata samu dala miliyan 2.5.
Kasashen da suka kai wasan daf da na kusa da na karshe, za a ba su dala miliyan 1.3,wadanda kuma suka fice a zagaye na 16 za a baiwa kowace kasa dala 800,000.
A matakin rukuni kuma wadanda suka kare a matsayi na uku zasu samu dala 700,000 yayinda na uku da na hudu a matakin rukuni kowanensu zai samu dala 500,000.
Source: LEADERSHIPHAUSA