Mai horas da ‘yan wasan kwallon kafa na Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Carlos Queiros, ya bayyana gamsuwar sa da kokarin ‘yan wasan sa kuma ya bayyana yadda a kullum yake alfahari da su.
Carlos ya bayyana cewa duk da barin wasan kwallon kafa na duniya da Iran din tayi amma ta baro wasan cikin mutunci da kuma dattako.
Kocin ya bayyana cewa ”Ina alfahari duk ‘yan wasa na suna da kyau, a baya na horas da ‘yan wasan kasashe irin su Chana, Afirka ta kudu, Amurka, Hadaddiyar daular larabawa amma yanzu ne nasan na samu ‘yan wasa na kwarai”
Kungiyar kwallon kasa ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran a wasan fitowa da guruf ne wasan kwallon kafa na duniya da ake gudanarwa a Qatar ne dai na tashi daya babu ko daya da Amurka.
Hakan ta sa a guruf din B Amurka da Ingila suka fito Iran kuma da Wales basu samu fitowa ba.
Bambancin wasan kwallon kafan duniya na 2022 da ssuran wasanni:
Wannan wasan kwallon kafan na duniya ya sha bambam da sauran wasannin kwallon kafa na duniya da aka dingi yi a baya, hada Iran, Amurka, Ingila da Wales a guruf daya ya sanya idanun duniya ya koma kallon wannan guruf a matsayin guruf din da yafi kowanne siyasa.
Duba da sabanin dake tsakanin musamman Iran da Amurka a siyasar duniya, tattare da cewa Amurka ta jima tana kakabawa Iran din takunkuma tattalin arziki dana shigara da magunguna.
Babban abinda ya dauki hankalin duniya shine yadda kafafen yada labarai mallakin Saudiyya da na kasashen turai irin su, Amurka, Ingila gami da Jamus suka dauki dakon yada furofagandoji a kan Iran din gaf da fara wasannin cin kofin duniyan.
Iran wacce makociyar Qatar ce kuma tana cikin mas daukan nauyin baki a wasannin na cin kofin duniya ta zargi wadancan kasashe da kokarin rikita ‘yan wasan ta ta hanyar amfani da farfaganda.