Birmingham City ta soke kwantiragin babban kocinta, Wayne Rooney bayan rashin tabuka abin azo a gani a gasar Championship.
Rooney ya samu nasara a wasanni biyu kacal cikin 15 da ya buga, sannan kungiyar ta sauka daga matsayi na shida zuwa na 20 a kan teburin gasar.
Kungiyar za ta yi sanarwar raba gari da Rooney a hukumance gami da tafiyarsa nan ba da jimawa ba.
A wani rahoto na daban a yayin da shekara ta 2023 ke bankwana a wannan makon, Kamfanin Jaridar LEADERSHIP HAUSA ya zakulo wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a wannan shekarar ta 2023 a bangaren wasabi.
Wasu daga cikin abubuwan da suka faru a bangaren wasanni a shekara mai karewa shi ne a ranar Laraba 6 ga watan Yuli na shekara ta 2023 aka kece-raini a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da takwararta ta Katsina United a wasan raba-gardama na neman tsallakewa zuwa gasar Firimiyar Nijeriya na kungiyoyi 8 da ke kira Super 8, inda a ciki za a dauki kungiyoyi hudu, biyu a Arewa, biyu a Kudu su dawo gasar Firimiyar.
A wasan karshe, Katsina United ta doke Kano Pillars da ci daya mai ban-haushi, inda Bictor Mbaoma ya zura kwallo a ragar Kano Pillars a bugun finareti, sai dai duk da an doke Pillars, kasancewar kungiyar DMD ta doke kungiyar EFCC ta Abuja, sai kungiyoyin Katsina United da Kano Pillars suka samu nasarar tsallakawa zuwa Firimiya.
DMD ta lallasa EFCC da ci 3-0, inda Kano Pillars ta kare da maki shida, Katsina United ta samu maki shida, DMD da EFCC suka samu maki uku-uku. A kakar bara ce dai kungiyar ta Kano Pillars ta yi rashin nasara, inda ta koma rukuni na biyu na gajiyayyu a gasar Nijeriya kuma a tarihin Kano Pillars, wadda aka kafa a 1990, sau uku tana buga gasar rukuni na biyu a 1994 da 1999 da kum
a bana.
Source: LEADERSHIPHAUSA