Belgium ta nada Domenico Tedesco a matakin sabon kociyanta
Hukumar kwallon kafa ta Belgium ta nada Domenico Tedesco a matakin sabon kociyan tawagarta.
Tsohon wanda ya horar da Schalke da Spartak Moscow da RB Leipzig, an haife shi a Italiya, yana da shedar zama dan kasa a Jamus.
Tedesco mai shekara 37, ya saka hannu kan kunshin kwantiragin da zai kare a karshen gasar nahiyar Turai, wato 2024 European Championship.
Ya maye gurbin Roberto Martinez, wanda ya yi ritaya, bayan fitar da Belgium a cikin rukuni a gasar kofin duniya, wanda ya yi shekara shida a aikin.
Tedesco zai fara aiki ranar 24 ga watan Maris a wasan neman gurbin shiga gasar kofin nahiyar Turai, inda Belgium za ta fafata da Sweden.
Ya koma Belgium wadda ta ci karo da cikas a gasar kofin duniya, bayan da ta je a matakin wadda aka sa ran za ta taka rawar gani.
Belgium ta halarci gasar a mataki ta biyu a fagen taka leda a duniya, amma aka yi waje da ita a cikin rukuni da cin wasa daya daga uku.
Martinez tsohon kociyan Swansea da Wigan da Everton nan da nan ya ajiye aikin bayan gasar kofin duniya, yanzu yana horar da tawagar Portugal.