Barcelona na son Bruno, Pochettino zai horas da Chelsea
Barcelona ta na so ta dauki dan wasan tsakiya na Brazil Bruno Guimaraes, sai dai kungiyar na ganin sai an bada kudi kusan yuro miliyan 100 ga Newcastle United kafin ta sayar da dan wasan mai shekara 25. (Times – subscription required)
Real Madrid na duba yiwuwar daukar dan wasan gaba na Brazil Roberto Firmino, mai shekara 31, wanda kwantiraginsa za ta kare daga Liverpool a kakar bana. (Fabrizio Romano)
Tsohon manajan Tottenham da Paris St-Germain Mauricio Pochettino dan shekara 51 ya sanya hannu kan kwantiragin shekara uku a matsayin sabon mai horaswa na Chelsea. (Guardian)
Brazil ta na kyautata zaton za ta iya shawo kan mai horas da Real Madrid Carlo Ancelotti don ya zama sabon mai horas da ‘yan wasan kasar. Zakarun ‘yan wasan na duniya sun kasance ba su da mai horas dasu tun barin Tite a watan Disamba bayan kammala wasan kofin duniya a Qatar. (Athletic – subscription required)
Mai yiwuwa Liverpool ta dauki Lazio da Sergej Milinkovic-Savic, mai shekara 28 a kan yuro miliyan 26m a yayin da kwantiragin dan wasan zata kare a shekarar 2024. (Calciomercato via Goal)
Damar da Manchester United ke da ita ta dauko Kim Min Jae mai shekara 26 da kuma Victor Osimhen mai shekara 24 daga Napoli na kara bayyana a fili.(Givemesport)
Newcastle United ta shiga sahun masu son dan wasan Napoli, Kim. (Fijaches – in Spanish)
Sheffield United ta na sanya ido kan dan wasan tsakiya na Nottingham Forest Lewis O’Brien mai shekara 24, wanda a yanzu haka ya ke bugawa DC United wasa. (Sun)
Crystal Palace ta kusa kammala shirin dauko dan wasan tsakiya na Bournemouth da kuma Colombia Jefferson Lerma mai shekara 28, a wannan kakar. (Fabrizio)