Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Turai, Aleksander Ceferin ya yi watsi da shawarar gudanar da gasar cin kofin duniya a duk bayan shekaru biyu-biyun, yana mai cewa bamu yarda ba saboda hakan zai rage armashin babbar gasar ta duniya.
Hukumar Kwallon Kafa ta duniya na yin nazari kan yiwuwar gudanar da gasar duk bayan shekaru biyu-biyu bayan da Saudiya ta fara neman haka a cikin watan Mayu.
Shi dai Ceferin na da ra’ayin cewa, gasar ta cin kofin duniya ta bamu daraja ne saboda yadda ake gudanar da ita duk bayan shekaru hur-hudu, abin da ya sa ake marmarinta.
Tun da aka kirkiro gasar a shekara ta 1930, kusan shekara 100 kenan, ake gudanar da ita duk bayan shekaru hur-hudu, in ban da shekara ta 1942 da kuma 1946 da aka samu akasi a dalilin yakin duniya na biyu.
Shugaban ya tabbatar da cewa ”bamu yarda da hakan bane domin kiyaye darajar da gasar take dashi” sa’annan da kuma tabbatar da yadda mutane ke mararin zagayowar kakar wasan a kowanne lokaci.
A wani labarin na daban kamfanin dilalncin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, jagoran juyin juya halin muslunci na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya jinjina wa ‘yan wasan kasar kan nuna kwazon da suka yi a gasar motsa jiki ta nakasassu ta duniya.
Ga matanin sakon:
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai
Ina godiya matuka da kuma yin jinjina ga ‘yan wasan Iran da suka nuna kwazo a a gasar motsa jiki ta nakasassu ta duniya wadanda suka faranta ran ‘yan kasarsu ta hanyar samun lambobin yabo na zinariya.
Sayyid Ali Khamenei
4 Satumba 2021