Atletico ta taka wa Real burki bayan cin wasa biyar a jere a La Liga
Atletico Madrid ta doke Real Madrid 3-1 a wasan mako na shida a La Liga da suka kara ranar Lahadi.
Ana take leda da minti hudu ne Atletico ta fara zura kwallo ta hannun Alvaro Morata, sannan minti 14 tsakani, Antoine Griezmann ya kara na biyu.
Real Madrid ta zare daya ta hannun Toni Kroos, saura minti 10 a tafi hutun rabin lokaci.
Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Atletico ta kara na uku ta hannun Morata, kuma na biyu da ya zura a raga a wasan.
Karon farko da aka doke Real a babbar gasar tamaula ta Sifaniya a bana, bayan da ta lashe dukkan karawa biyar a jere da fara kakar nan.
Da wannan sakamakon Real ta koma ta ukun teburi da maki 15 bayan wasa shida da fara kakar nan.
Barcelona ce ta daya mai maki 16 iri daya da na Girona, wadda take ta biyu.
Real ta ziyarci Atletico da rashin kokari a Champions League, wadda ta ci Union Berlin 1-0 a tsakiyar mako, kungiyar da ta fara buga gasar a karon farko a bana.
Kungiyar Sifaniya ba ta taka leda ba a wasan kamar yadda ta saba, sannan ‘yar damar makin da ta samu ba yawa a wasa da kungiyar Jamus.
Atletico ta taka rawar gani a gasar zakarun Turai, sai dai ta yi sakacin da Lazio ta farke kwallo da aka zura mata a lokacin ana daf da za a tashi daga wasan.
Wasa uku da suka buga a bara 2022/2023
Spanish La Liga Asabar 25 ga watan Fabrairun 2023
- Real Madrid 1 – 1 Atl Madrid
Copa del Rey Alhamis 26 ga watan Janairun 2023
- Real Madrid 3 – 1 Atl Madrid
Spanish La Liga Lahadi 18 ga watan Satumbar 2022
- Atl Madrid 1 – 2 Real Madrid
Real wadda karon farko da aka doke ta a wasannin bana a La Liga za ta karbi bakuncin Las Palmas ranar Laraba 27 ga watan Satumba.
Kwana uku tsakani za ta je gidan Girona a La Liga wasan mako na takwas, sannan ta ziyarci Napoli a wasa na biyu a cikin rukuni a Champions League ranar 3 ga watan Oktoba.