Kungiyar Aston Villa ta amince ta dauki aron tsohon dan wasan Liverpool Phillippe Coutinho aro daga Barcelona zuwa karshen kakar nan.
yarjejeniyar da ta’allak kan gwajin lafiya da kuma da samun umarnin aiki, ta bayar da damar kungiyar ta sayi dan wasan Brazil mai shekara 29.
Coutinho ya koma Barcelona a watan Janairun 2018 daga Liverpool kan kudi fan miliyan 142.
Haka zalika, bai yi tsammanin kawo wa Barcelona wani sauyi ba, shi yasa suke neman kai da shi.
Arsenal da Everton da Newcastle da kuma Tottenham na daga kungiyoyin da ke neman dan wasan.
BBChausa.