Arsenal ta dauki aron David Raya golan Brentford
Arsenal ta dauki aron David Raya mai tsaron ragar Brentford kan yarjejeniyar zuwa karshen kakar bana.
An kuma bai wa Gunners zabin sayen dan kwallon idan ya taka rawar gani da take bukata.
Raya, mai shekara 27, wanda zai sa riga mai lamba 22 zai kalubalanci Aaron Ramsdale a gurbin mai tsaron ragar Arsenal.
Ya buga karawa 11 ba tare da kwallo ya shiga ragarsa ba a kakar da ta wuce, wadda Brentford ta yi ta tara a teburin Premier League.
Gunners za ta buga Champions League a kakar nan a karon farko tun bayan 2017, wadda ta yi ta biyu a kakar da ta wuce.
Raya ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka biyu a Brentford da cewar za a iya tsawaita masa wata 12 idan ya taka rawar gani.
Golan ya koma Brentford daga Blackburn a 2019, lokacin da kungiyar take Championship.
Ya fara buga wa tawagar Sifaniya tamaula a karawar sadazumunta da ta ci Albania 2-1 a cikin watan Maris din 2022, yana cikin wadanda suka wakilci kasar a kofin duniya a Qatar a 2022.
Tottenham ta yi kokarin daukar mai tsaron ragar don maye gurbin had Hugo Lloris, amma ba ta samu daukar golan ba.
A watan nan Arsenal ta sayar da Matt Turner ga Nottingham Forest, wanda ya fara buga mata Premier League ranar Asabar da Arsenal ta ci 2-1.