Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal na ci gaba da haskawa a wannan kakar wasanni ta bana bayan doke abokiyar karawarta Sheffield United da ci 6 da babu a wasan da suka buga a ranar Litinin.
Kamar yadda leadership ta wallafa wannan nasarar da Arsenal ta samu ya sa ta ci gaba da zama a matsayi na uku, inda ta ke da tazarar maki daya tsakaninta da Manchester City da ke matsayi na biyu da kuma maki biyu tsakaninsu da Liverpool da ke jan ragamar gasar.
A wasan wanda aka buga a ranar Litinin Arsenal ta jefa kwallaye shida rigis ta hannun Martin Odegard, Martinelli, Kai Harverrz, Declan Rice da Ben White sai kuma Boygle wanda ya ci gidansu.
Da wannan ne Arsenal ta buga wasanni bakwai a jere a gasar Firimiyar Ingila ba tare da an doke ta ba, kuma ta jefa kwallaye 31 aka zura mata kwallo uku kacal a ragarta.
Karawar Manyan Kungiyoyin Kwallon Kafa Na Ingila
A wani labarin na daban Lahadin data gabatar ne manyan kungiyoyin kwallon kafa da ke da mazauni a daya daga cikin manyan biranen kasar Ingila suka kara da juna a wasan mako 27 na gasar Firimiya ta kasar Ingila.
Wasa tsakanin Manchester United da Manchester City yana matukar daukar hankalin masu sha’awar kallon kwallon kafa a fadin Duniya.
Duba da cewa duka manyan kungiyoyin biyu suna zaune ne a gari daya, wato Manchester, kuma dukkansu sun lashe manyan kofuna a fannin kwallon kafa kuma suna da manyan ‘yan wasa wadanda suka iya taka leda.
DUBA NAN: Babbar Alakar Da Najeriya Ta Kulla Da Qatar
Kungiyoyin biyu sun hadu har sau 189 a tarihi a mabanbantan kofuna da wasannin sada zumunta, inda Manchester United take kan gaba a samun nasarori da nasara 77, sun kuma yi kunnen doki a wasanni 59.