Kawo yanzu dai kofuna biyu ne suka rage da Arsenal ke fatan dauka a bana da ya hada da Premier League da kuma gasar cin kofin zakarun Turai na Champions League kafin kammala kakar wasa ta 2023 zuwa 2024. Yanzu saura wasa tara ya rage a karkare wasannin Premier League na bana, inda Arsenal take matakin farko da maki 64, iri daya da na Liberpool ta biyu sai kuma mai rike da kofin bara, Manchester City tana matsayi na uku a teburin da tazarar maki daya tsakaninta da Liberpool da kuma Arsenal.
Sai dai Arsenal da Liberpool da kuma Manchester City kowacce wasa 28 suka buga a Premier, bayan da aka fafata a FA Cup a karshen mako sai dai tuni Manchester City ta kai dab da karshe a FA Cup, bayan cin Newcastle United, ita kuwa Liberpool ta yi ban kwana da gasar, sakamakon da Manchester United ta doke ta 4-3.
Tun farko sun tashi 2-2 a Old Trafford ranar Lahadi daga nan suka shiga karin lokaci, inda kungiyar da Erik ten Hag ke jan ragama ta kai zagayen dab da karshe kuma a wa-tan gobe ne United za ta kece raini da Cobentry City mai buga Championship a dab da karshe a FA Cup a filin wasa na Wembley.
Ita kuwa Manchester City mai kofin bara na bakwai jimilla za ta buga wasan hamayya da Chelsea a watan goben a Wembley a zagayen dab da karshe amma dama tuni an fitar da Arsenaal a League Cup ranar Laraba 1 ga Nuwamba, bayan da West Ham United ta yi nasarar cin 3-1. Haka kuma Liberpool ce ta yi waje da Arsenal a FA Cup na kakar nan ranar 7 ga Janaiiru, bayan da aka ci Arsenal 2-0 har gida amma a gasar
Premier League, Arsenaal ta yi wasa 28 ta yi nasarar cin 20 da canjaras hudu aka doke ta fafatawa hudu da cin kwallo 70 aka zura mata 24 a raga da kuma maki 64.
Wadanda suke kan gaba a cin kwallaye a Premier League Erling Haaland Manchester City 18 Ollie Watkins Aston Billa 16 Mohamed Salah Liberpool 15 Dominic Solanke Bournemouth 15 Heung-min Son Tottenham 14 Jarrod Bowen West Ham United 12
Bukayo Saka Arsenal 13 Aledander Isak Newcastle United 12 Phil Foden Manchester City 11 Cole Palmer Chelsea 11 Wasannin mako na 30 a Premier League Ranar Asa-bar 30 ga watan Maris Newcastle United da West Ham Chelsea da Burnley
Tottenham da Luton Town Nottingham Forest da Crystal Palace Sheffield United da Fulham Bournemouth da Eberton Aston Billa da Wolberhampton Wanderers Brentford da Manchester United Ranar Lahadi 31 ga watan Maris Liberpool da Brighton & Hobe Albion Manchester City da Arsenal Wasannin da suka rage a gaban Arsenaal.
Yayin da ya rage saura wasanni tara Arsenal za ta buga a Premier League kafin karkare kakar bana da fafatawa biyu a Champions League saboda cikin watan Afirilu Arsenal za ta kara da Bayern Munich gida da waje a babbar gasar zakarun Turai ta bana, zagayen kusa da na kusa da na karshe.
Idan har Arsenal ta yi nasarar kai wa zagayen gaba, kenan tana da sauran wasa uku a gabanta da ya hada da na dab da karshe gida da da waje da kuma wasan karshe idan ta samu nasara.
Haka kuma tana da kwantan wasa daya kenan a Premier League da ya kamata ta kara da Chelsea ranar 16 ga watan Maris sai dai an dage wasan, sakamakon da Chelsea ta buga wasa da Leicester City a FA Cup, ta kuma kai zagayen dab da karshe za ta fuskanci Manchester City a watan gobe a Wembley.
Arsenal, wadda ta yi shekara 20 rabon ta dauki Premier League, ba ta taba lashe Champions League ba, amma kuma duk da haka kungiyar ta taba share kakar wasa 20 a jere tana zuwa gasar.
Wasannin da ke gaban Arsenal a yanzu haka Premier League Ranar Lahadi 31ga watan Maris 2024
Man City da Arsenal Premier League Ranar Laraba 3 ga watan Afirilu 2024, Arsenaal da Luton Premier League Ranar Asabar 6 ga watan Afirilu 2024. Brighton da Arsenal Champions League Ranar Talata 9 ga watan Afirilu 2024
Arsenal da Bayern Munich Premier League Ranar Lahadi 14 ga watan Afirilu 2024
Arsenal da Aston Billa Champions League Ranar Laraba 17 ga watan Afirilu 2024
Bayern Munich da Arsenal Premier League Ranar Asabar 20 ga watan Afirilu 2024
Wolbes da Arsenaal Premier League Ranar Asabar 27 ga watan Afirilu 2024
Tottenham da Arsenal Premier League Ranar Asabar 4 ga watan Mayu 2024
Arsenal da Bournemouth Premier League Ranar Asabar 11 ga watan Mayu 2024
Man Utd da Arsenal Premier League Ranar Lahadi 19 ga watan Mayu 2024
Arsenal da Eberton Arsenal a Champions League. Arsenal ta kawo matakin kusa da na kusa da na karshe a Champions League a bana, bayan da ta buga karawa takwas, wadda ta yi nasara biyar da canjaras daya da rashin nasara biyu.
Kungiyar ta ci kwallo 17 aka zura mata biyar a raga, wadda ta yi nasara a kan FC Porto a zagayen ‘yan 16 a gasar ta zakarun Turai hakan yana nufin Arsenal ta kai matakin kusa da na kusa da na karshe a Champions League a karon farko tun kakar wasa ta shekarar 2009 zuwa 2010.
Sannan Arsenal ta kawo karshen rashin nasara bakwai a jere a zagayen ‘yan 16 a gasar ta zakarun Turai kuma Arsenal ta taba jera kaka 20 tana buga Champions League, wadda ta kai wasan karshe daya daga ciki, amma ba ta taba lashe kofin ba.
DUBA NAN: Ban Bar Jam’iyyar LP Ba– Peter Obi
Arsenal ta buga Champions League ko European Cup karo 209 da yin nasara 106 da canjaras 44 da rashin nasara 59 ta zura kwallo 349 aka zura mata 223 a raga a gaba daya wasannin.