Tawagar kwallon kafa ta kasar Brazil ta ajiye dan kwallon Manchester United, Antony daga tawagarta, wanda ake zargi da cin zarafin tsohuwar budurwarsa a birnin Soa Paulo. Hukumar kwallon kafa Brazil ta ce dan wasan mai shekara 23 ba zai buga mata karawar ba, bayan da ake zarginsa, wanda kawo yanzu tuni aka fara bincike akan zargin.
Ranar Litinin wata jarida ta Brazil ta wallafa labarin zargin cin zarafin da Anthony ya yi wa tsohuwar budurwarsa kuma tuni ‘yansanda a Sao Paulo da na Greater Manchester na bincikar lamarin, yayin da dan kwallon ke musanta zargin.
Ana zargin Antony da farwa tsohuwar budurwarsa, Gabriela Caballin wacce ya yi wa gware da ka a wani otal a Manchester ranar 15 ga watan Janairun wannan shekarar da muke ciki. Hakan ya sa ta ji ciwo a kanta da ta kai likitoci suka yi mata aiki sannan ta kuma yi zargin cewa ya naushe ta a kirji da ta kai ya yi mata illa da sai da aka yi mata aiki a cewarta.
Antony ya bayyana a wata sanarwa cewar alakarsa da tsohuwar budurwarsa sun saba yin hatsaniya, amma bai taba dukanta ko cin zarafinta ba, sannan ya taba fitar da wata sanarwa a cikin watan Yuni cewar tsohuwar budurwarsa na yi masa zargin karya na cin zarafi.
Manchester United ta ce babu abin da za ta ce kan batun, sai dai lamarin Antony ya taso ne bayan da kungiyarta sanar da cewar dan wasanta Mason Greenwood zai bar kungiyar, bayan wata shida da aka zarge shi da cin zarafi.
Cikin zargin da aka soke kan Greenwood har da batun fyade da cin zarafi, sai dai tuni dan wasan mai shekara 21 a duniya ya koma Getafe ta Sifaniya da zai yi mata wasannin aro.
Brazil ta maye gurbin Antony da dan kwallon Arsenal, Gabriel Jesus, wanda ya dawo daga jinya a wasan neman gurbin shiga gasar kofin duniya da za ta kara da kasashen Bolibia da kuma Peru.
Source: LEADERSHIPHAUSA