An Sanar Da Yan Wasan Da Za su Bugawa Najeriya Wasa A Fafatawarta Da Ghana.
Tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, Super Eagles ta bayyana kashin farko na ‘yan wasan da za su buga mata fafatawa da Ghana a wasan neman cancantar shiga Kofin Duniya na Qatar 2022. Matashin ɗan wasan gaba na Leicester City Ademola Lookman na cikin tawagar, inda zai saka wa ƙasarsa riga a karon farko.
A kwanan nan ne hukumar ƙwallon ƙafa ta Fifa ta bai wa Lookman damar buga wa Najeriya wasa bayan fara saka wa Ingila riga.
Kazalika, tawagar ta ‘yan ƙwallo 32 ta ƙunshi matashi Akinkunmi Amoo, wanda ya wakilci ƙasar a gasar Kofin Duniya na ‘yan ƙasa da shekara 17.
Za a fara buga wasan ne a ranar 25 ga watan Maris a Ghana kafin a buga wasa na biyu a Najeriya a 29 ga wata da zimmar fitar da wadda za halarci gasar da ƙasar Qatar za ta karɓi baƙunci karon farko a tarihinta.
Sauran taurarin da ke cikin tawagar sun haɗa da kyaftin Ahmad Musa, da William Ekong, da Wilfred Ndidi, da Moses Simon, da Kelechi Iheanacho.