An Gusa Gasar AFCON Ta Badi Zuwa Janairun 2024.
Hukumar kwallon kafa ta Afrika, ta ce za A fara gasar cin kofin kwallon kafa ta nahiyar ta badi a Ivory Coast daga watan Janairu zuwa Fabarairu na shekarar 2024.
Shugaban hukumar ne Patrice Motsepe, ya bayyana hakan a birnin Rabat a daura da gasar cin kofin kwallon kafa ta Afrika ta mata dake gudana a Moroko.
Mista Motsepe, ya ce an gusa lokacin ne saboda dalilin yanayi inda za’a fara gasar ta 2023 daga watan Janairun 2024, kamar yadda kwamitin zartaswa na hukumar ya amince yayin taronsa.
Tunda farko dai an tsara gudanar da gasar daga watan Yuni zuwa July na 2023.
Shugaban hukumar ya kuma ce gusa lokacin gudanar da gasar ba shi da wata alaka da shirye shiryen karbar gasar da kasar Ivory Coast ke yi, inda ya jinjina wa kasar game da ayyukan da take gudanarwa domin karbar gasar ta badi.
READ MORE : Za a maido da dangantaka tsakanin Poland da gwamnatin Sahayoniya.
Saidai kuma shugaban hukumar bai yi bayyani ba game da tambayar da aka masa kan cewa ko matakin zai kuma shafi gasar ta 2025 da za’a yi a Guinea saboda duk kusan a yanayi guda ne za’ayi gasar.