Fitaccen dan kwallon kafan Najeriya, Ahmad Musa ya yada wani bidiyon sabuwar cibiyar wasannin da ya gina a jihar Kaduna..
Cibiyar wasannin ta zamani na da ramin ninkaya, wajen motsa jiki, filin wasan tennis da dai sauran nau’ikan wasanni.
Ahmad Musa na daya daga cikin attajiran ‘yan wasan kwallon kafa a Najeriya da ama Afrika da ke zuba kudadensu a fannin wasanni da ci gaban jama’a.
Fitaccen dan kwallon Najeriya, Ahmad Musa ya bude wata katafariyar cibiyar wasanni a jihar Kaduna, inda ya yada bidiyon cikin cibiyar.
Matashin mai shekaru 30 yana ci gaba da lashe zukatan jama’a a Najeriya da ma sauran kasashen duniya bisa yadda yake yiwa al’ummarsa hidima ta hanyoyi da yawa.
Babu shakka Ahmad Musa na daya daga cikin attajiran ‘yan wasan kwallo a Afrika duba da irin abubuwan da yake yi a kasa Najeriya.
Ahmad Musa dai ya mallaki manyan gidaje a Najeriya da ma kasashen waje, kuma yana matukar alfahari da mallakar manyan motoci zafafa masu tsada.
A ina wannan katafariyar cibiya take? Wannan cibiya dai ya gina ta ne a Old Kamazo, Janruwa Layout kusa da babban titin Yakowa da ke birnin Kaduna a Najeriya.
Kamar yadda ya nuna a bidiyon da ya yada a Twitter, akwai ramin ninkaya, filin kwallon kafa, teburin wasan tennis, wurin motsa jiki, filin wasan tennis, na kwallon kwando, volley da dai sauransu.
Ahmad Musa ya kasance dan wasan kwallon kafa a wata kulob din kasar Turkiyya mai suna Sivasspor kuma yana bugawa gida Najeriya duk sadda bukatar hakan ta taso.
Ya zuwa yanzu ya buga wasanni 107, kuma ya sha kwallaye 16, kana ya lashe gasar cin kofin nahiyar Afrika ga Najeriya.
Ahmad Musa ya ginawa talakawa katafariyar makaranta a Jos
A wani labarin kuma, Ahmad Musan dai ya gina wata katafariyar makaranta domin tallafawa talakawa da kananan yara a jihar Filato.
Ahmad Musa ya sha bayyana irin ayyukan da yake yiwa al’ummarsa bayan da ya samu sanuwa a duniyar kwallon kafa a duniya.
A bidiyon da ya yada, an ga katafariyar makarantar mai bene hawa biyu da ya gina, ya ce kuma matakin na kasa da kasa ne, ta samu aiki mai inganci.