AFCON 2021 _ Turmutsitsi ya yi ajalin mutane a filin wasa a Kamaru
Aƙalla mutum shida aka bada rahoton sun mutu sannan da dama sun samu raunika sakamakon wani turmutsitsi da ya auku a wajen filin da ake buga gasar cin kofin nahiyar Afirca ta Afcon a Kamaru.
Hotunan bidiyo sun nuna yadda ‘yan kallo suka rinƙa kokowar shiga fili wasa na Paul Biya da ke birnin Yaounde.
Naseri Paul Biya, wanda shi ne gwamnan yankin tsakiyar Kamaru, ya ce akwai yiwuwar a samu karin mutanen da abin ya shafa, a cewar kamfanin labarai na AP.
Wani rahoton kuma na cewa akwai yara da dama da suka suma.
Filin wasan na iya daukar mutum dubu 60, amma saboda matakan da ake ɗauka saboda annobar korona ba a yarda a haura kashi 80 cikin 100 na wannan adadin ba.
Jami’ai sun ce mutum dubu 50 ne suka yi kokarin shiga filin wasan domin kallo.
Malaman jinya Olinga Prudence ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na AP cewa, wasu daga cikin mutanen da suka jikkata na cikin yanayi na galabaita.
Hukumar kwallon kasashen Afirka, CAF a wata sanarwa ta ce tana bincike kan lamarin domin samun ƙarin bayanai kan ainihin abin da ya faru.